ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA KA JI DAƊIN KARANTA LITTAFI MAI TSARKI
Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwata?
Littafi Mai Tsarki ba kamar sauran littattafai ba ne. Yana ɗauke da shawarwari daga wurin Mahaliccin mu. (2 Timotawus 3:16) Saƙon da ke cikinsa zai iya motsa mu mu yi wasu canje-canje a rayuwarmu. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce, “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” (Ibraniyawa 4:12) Yana da ikon inganta rayuwarmu a hanyoyi biyu. Yana ba mu shawarwari a kan yadda za mu bi da rayuwarmu na yau da kullum kuma yana taimaka mana mu san Allah sosai da alkawuransa.
Yana inganta rayuwarmu a yanzu. Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu bi da matsalolin mu. Yana ba da shawarwari masu kyau a kan waɗannan batutuwan.
-
Dangantakarmu da mutane.—Afisawa 4: 31, 32; 5: 22, 25, 28, 33. -
Tunaninmu da kuma lafiyar jikinmu.
—Zabura 37:8; Misalai 17:22. -
Ɗabi’a.
—1 Korintiyawa 6: 9, 10. -
Tattalin arziki.
—Misalai 10:4; 28:19; Afisawa 4:28. *
Wasu ma’aurata a Asiya da ba su jima da yin aure ba sun amfana sosai daga bin shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kamar sababbin ma’aurata da yawa, su ma sun yi fama da kurakuren juna da kuma yadda za su riƙa tattauna da juna. Sai suka soma bin shawarar Littafi Mai Tsarki. Mene ne sakamakon? Maigidan mai suna Vicent ya ce: “Karatun Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in bi da matsalolin aurenmu a hanyar da ta dace. Yin amfani da shawarar Littafi Mai Tsarki ya sa mu farin ciki a rayuwa sosai.” Matarsa mai suna Annalou ta ƙara da cewa: “Karanta labaran mutanen da ke Littafi Mai Tsarki sun taimaka mana. Yanzu ina jin daɗin aurenmu kuma na gamsu da maƙasudanmu.”
Sanin Allah. Ban da abin da Vicent ya ce game da aure, ya kuma ce: “Karanta Littafi Mai Tsarki ya sa na kusaci Allah fiye da dā.” Abin da Vicent ya ce yana da muhimmanci sosai domin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka san Allah. Ta hakan, za ka amfana daga bin shawarwarinsa kuma za ka ɗauke shi a matsayin abokinka na kud da kud. Za ka ga cewa ya yi bayani game da yadda duniyar nan za ta kasance a nan gaba kuma a wannan lokacin ne za ka ji daɗin “hakikanin rai” wadda ba za ta ƙare ba. (1 Timotawus 6:19) Babu wani littafin da zai iya amfanar ka kamar wannan.
Idan ka soma karanta Littafi Mai Tsarki, kai ma za ka inganta rayuwarka kuma ka kusaci Allah sosai. Babu shakka, za ka iya yin tambayoyi da yawa yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki. Idan haka ne, ka kasance da irin halin wani Bahabashe da ya yi rayuwa shekaru 2,000 da suka shige. Wannan mutumin yana da tambayoyi da yawa game da Littafi Mai Tsarki. Da aka tambaye shi ko ya fahimci abin da yake karantawa, sai ya ce: “Yaya zan iya, sai ko wani ya bishe ni?” * Bayan hakan, sai ya ce wa wani malami wanda mabiyin Yesu ne mai suna Filibus ya fahimtar da shi a kan abin da yake karantawa. (Ayyukan Manzanni 8:
Ka kalli bidiyon nan Ta Yaya Za Mu San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne? don sani ko ya kamata ka gaskata da Littafi Mai Tsarki. Za ka iya samun sa idan ka yi scan ɗin alamar nan ko kuma ka duba dandalin jw.org/ha, ƙarƙashin LITTATTAFAI > BIDIYO > LITTAFI MAI TSARKI.
^ sakin layi na 8 Don ƙarin bayani a kan shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki, ka shiga dandalin jw.org/ha. Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AN AMSA TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI.
^ sakin layi na 11 Ka kuma duba talifin nan “Rashin Fahimta Ƙaramar Matsala Ce?” a shafi na 14.