LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE
Ina Son Kwallon Baseball Fiye da Kome!
-
SHEKARAR HAIHUWA: 1928
-
ƘASAR HAIHUWA: KWASTA RICA
-
TARIHI: INA SON YIN WASANNI DA KUMA CĀCA
RAYUWATA A DĀ
Na girma a babban birnin Puerto Limón, da ke ƙasar Kwasta Rica. Iyayenmu sun haifi yara takwas kuma ni ne na bakwai. Mahaifina ya rasu sa’ad da nake ɗan shekara takwas. Bayan haka, mahaifiyarmu ce ta rene mu ita kaɗai.
Na shaƙu da buga ƙwallon baseball sosai kuma na so wasan tun ina yaro. Na shiga wata ƙungiya da ke buga ƙwallon baseball sa’ad da nake matashi. Da na kai shekara 20, sai aka gayyace ni in shiga ƙungiyar ƙwararrun ‘yan wasan baseball a ƙasar Nicaragua. Amma a lokacin, mahaifiyata ba ta da lafiya sosai kuma ni ne nake kula da ita. Don haka, sai na ƙi amincewa da gayyatar don ba na so in je ƙasar Nicaragua. Bayan wasu lokuta, sai aka zaɓe ni tare da wasu ‘yan wasa don mu buga wa ƙasar Kwasta Rica ƙwallon baseball. Sai na amince. Na yi wa Kwasta Rica wasa daga shekara ta 1949 zuwa 1952, kuma na yi wasanni dabam-dabam a ƙasar Cuba da Meziko da kuma Nicaragua. Na iya wasan sosai, zan iya buga wasanni guda 17 ba tare da yin kuskure ba. Idan ‘yan kallo suna ihu suna kiran sunana, hakan yana sa ni farin ciki sosai!
Amma, abin baƙin ciki shi ne na yi rayuwar da ba ta dace ba. Ina da budurwa guda ɗaya, amma duk da hakan, ina neman wasu mata kuma nakan yi maye da giya sosai. Wata rana da na farka da safe, ban iya tuna yadda na zo gida ba domin sabar yadda na bugu da giya a daren! Ƙari ga haka, ina yin cāca dabam-dabam da dai sauran su.
Yayin da nake waɗannan abubuwan, sai mahaifiyata ta zama Mashaidiyar Jehobah. Ta yi ƙoƙari ta sa in amince da abin da ta yi imani da shi amma ba ta yi nasara ba domin ba abin da na sa a gaba sai ƙwallon baseball. Idan ina wasa a fili, ba na jin yunwa ko da lokacin cin abinci ya yi domin gabaki ɗaya hankalina yana kan wasan! Ina son buga ƙwallon baseball fiye da kome!
Amma, sa’ad da na kai shekara 29, na samu rauni a filin wasa sa’ad da nake ƙoƙarin kama ƙwallo. Bayan na sami sauƙi, sai na daina buga wa kulob wasa. Amma na buɗe wani ƙaramin
ƙungiya a kusa da gidana don in riƙa koya wa wasu ƙwallon baseball.YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA
A shekara ta 1957, an gayyace ni zuwa taron yanki na Shaidun Jehobah wanda za a yi a wani filin wasa da na taɓa yin ƙwallon baseball a ciki. Da na je, na lura cewa halayen mutanen da suke wajen ya bambanta sosai da na masu kallon wasa. Abin da na gani ya motsa ni in soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro.
Abubuwan da na koya a Littafi Mai Tsarki sun burge ni sosai. Alal misali, Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa a kwanaki na ƙarshe, za su yi wa’azi game da Mulkin Allah a dukan faɗin duniya. (Matta 24:14) Na kuma koya cewa Kiristoci na gaskiya za su yi wa’azi ba don kuɗi ba. Domin Yesu ya ce: “Kyauta kuka karɓa, sai ku bayar kyauta.”
Yayin da nake nazarin Littafi Mai Tsarki, ina gwada abin da ya ce da kuma abin da Shaidun Jehobah suke yi. Yadda suke iya ƙoƙarinsu wajen yin wa’azin Mulkin Allah a ko’ina ba tare da gajiya ba yana burge ni sosai. Na ga cewa suna yin abin da Yesu ya ce Kiristoci su yi, wato su yi wa’azi kyauta. Da na karanta abin da Yesu ya ce a Markus 10:21 cewa: “Ka zo ka bi ni,” sai na yanke shawara cewa zan zama Mashaidin Jehobah.
Amma bai kasance mini da sauƙi in yi wasu canja-canjen da suka dace ba. Alal misali, kowane sati ina zuwa yin cāca kuma na yi shekaru da yawa ina yin hakan. Sai na karanta a Littafi Mai Tsarki cewa Allah ba ya ƙaunar masu haɗama da masu bauta wa allahn “sa’a da na ƙaddara.” (Ishaya 65:
A ranar da na yi baftisma a wani babban taron Shaidun Jehobah, na fuskanci wani jarrabawar ta nuna ko na riga na koyi wannan “sabon halin” da ya kamata na kasance da shi. (Afisawa 4:24) A ranar da yamma, na koma otel ɗin da nake kwana kuma na tarar da budurwata ta dā tana jira na a bakin ƙofar ɗakina. Sai ta ce mini, “Ya dai Sammy, ka zo mu ji daɗin rayuwa!” Nan da nan sai na ce mata, “A’a!” Na gaya mata cewa yanzu ni ina rayuwa ne bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (1 Korintiyawa 6:18) Sai ta ce, “Me ka ce?” Bayan haka, sai ta soma cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da lalata ba daidai ba ne kuma ta nace da mu ci gaba da soyayyarmu. Sai na tafi na shiga ɗakina kuma na rufe ƙofar. Yanzu ina farin ciki cewa tun da na zama Mashaidi a shekara ta 1958, na ci gaba da yin abubuwan da suka dace a rayuwata.
YADDA NA AMFANA
Ina ji kamar in rubuta a cikin littafi game da duka amfanin da na samu don na bi ja-gorar Littafi Mai Tsarki! Wasu daga cikin amfanin su ne na samu abokan kirki, rayuwata ta ƙara kasancewa da ma’ana kuma ina farin ciki sosai.
Har yanzu ina son buga ƙwallon baseball amma ba kamar dā ba. Na yi suna da kuma kuɗi sosai sa’ad da nake ƙwallon baseball amma waɗannan abubuwan ba na ƙwarai ba ne. Dangantakata da Jehobah da kuma ‘yan’uwa su ne na ƙwarai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:17) Yanzu ina ƙaunar Jehobah da kuma mutanensa fiye da kome!