Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

Ana Taimaka wa Mutane Su Iya Karatu

Ana Taimaka wa Mutane Su Iya Karatu

 Wani mai suna Agostinho da ke zama a Brazil ya ce: “Na yi girma wurin da ake noma a kasar, mu talakawa ne sosai. Na bar makaranta don in yi aiki in biya bukatun iyalinmu.” Agostinho ya koyi yin karatu da rubutu sa’ad da ya kai shekara 33. Ya ce: “Iya karatu da rubutu ya sa mutane su rika daraja ni.”

 Agostinho yana cikin mutane da yawa da Shaidun Jehobah suka koya wa yin karatu da rubutu cikin shekaru 70 da suka shige. Me ya sa Shaidun Jehobah suke koya wa mutane karatu? Ta yaya mutane suka amfana daga koyan rubutu da karatu?

Yana Wuya Ka Koyi Abu Ba Tare da Iya Karatu Ba

 A shekara ta 1935, Shaidun Jehobah suna wa’azi a kasashe 115. Don su yi wa mutane da suke yaruka dabam-dabam wa’azi, masu wa’azi a kasar waje suna saka musu jawaban Littafi Mai Tsarki da aka fassara kuma aka dauka a faifai. Ban da haka, a wasu lokuta suna ba mutane littattafanmu a yaruka dabam-dabam. Ko da yake mutane da yawa sun nuna suna son sakon Littafi Mai Tsarki, da yawa a cikinsu ba sa koyan wani abu don ba su iya karatu ko rubutu ba.

 Da yake mutane ba su iya karanta Littafi Mai Tsarki da kansu ba, suna fama ne su koyi yadda za su bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarsu. (Yoshuwa 1:8; Zabura 1:​2, 3) Ƙari ga haka, suna fuskantar matsaloli wajen cika hakkinsu a matsayinsu na Kiristoci. Alal misali, idan iyaye ba su iya karatu ba, zai yi musu wuya su koyar da yaransu. (Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7) Kuma zai yi ma wadanda suka zama Shaidu ba da dadewa ba wuya su yi amfani da Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke koyar da mutane.

An Soma Koyar da Mutane

 Tun daga shekara ta 1940 zuwa 1959 Dan’uwa Nathan H. Knorr da Milton G. Henschel da suke ja-goranci a kungiyar Jehobah a wannan lokacin sun yi tafiya zuwa kasashe dabam-dabam don su tsara yadda za a rika wa’azi. A kasashe da mutane da yawa ba su iya rubutu da karatu ba, an karfafa ’yan’uwan da ke reshen ofishinmu cewa a kafa aji a ikilisiyoyi don koyar da mutane karatu da rubuta.

An fitar da littafin da zai taimaka wa mutane su koyi karatu a yaren Cinyanja a taron da aka yi a birnin Chingola da ke Zambiya, a shekara ta 1954

 An ba ’yan’uwa umurni daga reshen ofishinmu game da yadda za su rika gudanar da ajin. A wasu kasashe da gwamnati ta riga ta kafa tsarin koyar da mutanen, muna bin wannan tsarin. Alal misali, a kasar Brazil, gwamnati tana tura wa reshen ofishinmu littattafai da abubuwan koyarwa, su kuma sai su tura zuwa ikilisiyoyi. A wasu kasashe kuma, Shaidu ne suka tsara yadda za su rika koyar da mutane.

 Kowa yana iya halartan ajin koyan rubutu da karatu. An kafa wannan ajin ne don a koya wa mutanen yadda za su rika karatu a yarensu, ko da hakan yana nufi cewa za a rika koyarwar a yaruka dabam-dabam a ikilisiya guda.

Makarantar da Ke Taimaka wa Mutane

 Ta yaya mutane suka amfana daga wannan makarantar? Wata Mashaidiya daga Meziko ta ce: “Yanzu ina fahimta sakon Littafi Mai Tsarki kuma hakan yana ratsa zuciyata. Iya karatu ya taimaka mini in rika tattaunawa da makwabtana, kuma ya taimaka mini in yada sakon Littafi Mai Tsarki ga mutane da yawa.”

 Wannan makarantar ba koya wa mutane sanin sako Littafi Mai Tsarki kawai ya yi ba. Wani mai suna Isaac daga Burundi ya ce: “Koyan rubutu da karatu ya taimaka mini in koyi aikin gini. Yanzu aikin gini nake yi kuma ina yin ja-goranci a wasu manyan aikin gine-gine.”

Ana koya wa ’yan’uwa karanta yaren Chichewa a Majami’ar Mulki a birni Lilongwe da ke Malawi, a shekara ta 2014

 Wata mai suna Jesusa daga Peru tana da shekara 49 sa’ad da ta soma koyan karatu da rubutu. Ta ce: “Da yake ni matar aure ce ina bukatar in san farashi da kuma sunayen abubuwa a kasuwa. A dā, hakan yana mini wuya. Wannan makarantar ta taimaka mini in kasance da gaba gadi sa’ad da nake sayayya a kasuwa.”

 Shekaru da yawa yanzu, hukumomi a kasashe da yawa suna yaba wa Shaidun Jehobah don kokarin da suke yi su koya wa mutane rubutu da karatu. Har a yau Shaidun Jehobah suna koya wa mutane rubutu da karatu, kuma suna yin amfani da kayan aiki da aka inganta. Kari ga haka, sun buga mujallu kusan miliyan 224 a yaruka 720 don su taimaka wa mutane su koyi rubutu ko karatu ko kuma su taimaka wa masara ilimi. *

^ Alal misali an wallafa kasidar nan Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa a yaruka 123 da kuma kasidar nan Ka Saurari Allah a yaruka 610.