Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

Shin Shaidun Jehobah a Kasar Niyu Zilan Kiristoci Ne na Gaskiya Masu Son Zaman Lafiya?

Shin Shaidun Jehobah a Kasar Niyu Zilan Kiristoci Ne na Gaskiya Masu Son Zaman Lafiya?

 A ranar 21 ga Oktoba, 1940, kasar Niyu Zilan ta sanar da cewa Shaidun Jehobah kungiya ce mai hadari, kuma tana iya jawo matsaloli ga al’umma. Duk da cewa matakin da gwamnatin ta dauka ya jawo ma Shaidun Jehobah matsaloli da yawa, amma ba su karaya ba. Alal misali, sun ci gaba da yin tarukan ibadar su duk da cewa hukumomi za su iya kama su.

 Maigidan ’yar’uwa Mary mai suna Andy Clarke, wanda ba Mashaidin Jehobah ba ne, ya lura da yadda ta ci gaba halartan taro duk da barazanar da aka yi musu. Ya ji tsoro cewa za a kama matarsa idan ta halarci taro. Sai ya soma raka matarsa zuwa taro, duk da cewa ba ya yin hakan a dā. Ya ce wa Mary, “Idan suna so su kama ki, sai sun kama ni ma!” Tun daga lokacin, Andy ya ci gaba da halartan taro da matarsa. A kwana a tashi, shi ma ya yi baftisma. Ko da yake an tsananta wa Shaidun Jehobah da yawa a Niyu Zilan a lokacin Yakin Duniya na biyu, da yawa daga cikinsu kamar Mary sun jimre da aminci.

Sun Sami Ci-gaba Duk da Cewa An Tsare Su

 Wata rana ’yan sanda suka kama John Murray mai shekaru 78 sa’ad da yake wa’azi gida-gida. Kotu ta kama shi da laifin saka hannu a ayyukan kungiya mai hadari. An kama Shaidun Jehobah da yawa ma aka kai su kotu; wasu an ci su tara, wasu kuma an saka su a kurkuku har tsawon watanni uku.

 Shaidun Jehobah sun ki shiga aikin soja saboda imaninsu. (Ishaya 2:⁠4) Saboda haka, an tsananta musu sosai a lokacin yakin sa’ad da aka kira su su shiga soja. Da yake sun ki shiga soja, an tsare wajen 80 daga cikin su a wani sansani a lokacin yakin. ’Yan’uwan sun ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki duk da wulakancin da aka yi musu da kuma tsananin sanyi a cikin sansanin.

 Shaidun da ke sansanin sun soma tsara ayyukan ibada nan da nan. Sun yi taro da kuma wa’azi a matsayin ikilisiya. A wasu sansanin ma an yarda wa Shaidun su yi manyan taro da yawa sa’ad da gandirobobi suke gādin su. Wasu daga cikin fursunoni a sansanin sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma an yi musu baftisma a wurin.

Shaidun Jehobah da ake tsare a sansani suna yin taron Makarantar Hidima ta Allah

 Bruce, dan Mary da Andy na karshe da aka ambata a baya ya dauki lokacin da ya yi a sansanin a matsayin damar kara koya game da Allah. Ya tuna abin da ya faru kuma ya ce: “Ya yi min kamar na je makaranta ne domin nakan tattauna sosai da kwararrun ’yan’uwa kuma nakan koyi abubuwa da yawa daga wurin su.”

 A 1944, gwamnati ta so ta saki wasu da ke sansanonin tsare mutane amma hukumomin sojoji sun ki domin a cewarsu, idan aka saki Shaidun Jehobah, za su ci gaba da yin wa’azi. Rahoton ya ce: “Ci gaba da tsare su zai iya dan rage kwazonsu, amma ba zai taba canja ra’ayinsu ba.”

Su Ba Hadari Ba Ne ga Jama’a

Yadda labarin hana Shaidun Jehobah yin wa’azi a kasar ya bazu, ya sa wasu mutane sun soma marmarin koya game da Shaidun Jehobah. A kwana a tashi, mutane da yawa suka gano cewa Shaidun Jehobah ba hadari ba ne ga jama’a ko kadan. Sun ga cewa Shaidun Jehobah  Kiristoci ne masu neman zaman lafiya kuma ba sa cutar kowa. A sakamakon haka, yawan Shaidun Jehobah ya karu daga 320 a 1939 zuwa 536 a 1945!

 A wasu lokuta, wasu jami’an gwamnati sukan gano cewa hana Shaidun Jehobah yin wa’azi da aka yi bai dace ba. Wani alkali da aka kai masa karar wani dan’uwan da yake wa’azi ya yi watsi da karar. Ya ce: “Bisa ga ra’ayina da kuma yadda na fahimci doka, wauta ce a ce mutum ya aikata laifi domin kawai yana ba mutane Littafi Mai Tsarki.”

 A karshen yakin, sa’ad da aka bar Shaidun Jehobah su soma yin wa’azi a sake, sai suka kara kwazo a taimaka wa mutane su koya game da Mulkin Allah. A 1945, an rubuta wasika ga dukan ikilisiyoyi a Niyu Zilan kuma wasikar ta ce: “Yayin da kuke wa’azi, kowa ya zama mai fara’a, mai alheri da kuma mai magana ga mutane cikin basira. Ku guji gardama da tashin hankali. Ku tuna cewa mutanen da muke musu wa’azi suna imani da koyarwar addininsu kuma suna rayuwa bisa ga koyarwarsa. . . . Da yawa daga cikin su ‘tumakin’ Ubangiji ne, kuma dole mu taimaka musu su san Jehobah kuma su shiga mulkinsa.”

 A yau, Shaidun Jehobah a Niyu Zilan suna ci gaba da yin wa’azi ga ’yan kasarsu da kuma bakin da suka je yawon bude ido. Akwai ranar da Shaidun Jehobah guda 4 a Turangi suka yi wa’azi ga baki 67 daga kasashe 17 a cikin ’yan awoyi kawai!

 A bayyane yake cewa mutanen Niyu Zilan sun gano cewa Shaidun Jehobah Kiristoci ne masu son zaman lafiya da suke bin abin da Littafi Mai Tsarki ya fada. Ana yi wa darurruwan mutane baftisma a matsayin Shaidun Jehobah a kowace shekara. Zuwa shekara ta 2019, Shaidun Jehobah fiye da 14,000 ne suke bauta wa Jehobah da farin ciki a wannan kasar da ke kudancin duniya.

Wani taro, bayan da aka hana ayyukan Shaidun Jehobah a 1940

Dakin kurkuku na mutum daya a sansanin tsare mutane da ke North Island a Niyu Zilan

Sansanin Hautu da ke North Island, a Niyu Zilan

A 1949, wasu Shaidun Jehobah da aka tsare domin sun ki shiga soja saboda imaninsu