Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hagu: Mahaukaciyar guguwa na Ian, a Florida, Amirka, a watan Satumba 2022 (Sean Rayford/Getty Images); tsakiya: Mata da danta suna gudun hijira, a Donetsk, Yukiren, a watan Yuli 2022 (Alex Chan Tsz Yuk/SOPA Images/LightRocket via Getty Images); dama: Ana yi wa mutane da yawa gwajin cutar korona, a Beijing, Caina, a watan Afrilu 2022 (Kevin Frayer/Getty Images)

KU ZAUNA A SHIRYE!

2022: Shekarar Damuwa da Hargitsi—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

2022: Shekarar Damuwa da Hargitsi—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 A 2022, mun yi ta jin labarai game da yaki da faduwar tattalin arziki da kuma balaꞌoꞌi. Littafi Mai Tsarki ne kawai ya bayyana ainihin abin da ya sa abubuwan nan suke faruwa.

Ainihin dalilin da ya sa abubuwan nan suka faru a 2022

 Abubuwan da suka faru shekarar da ta shige, sun kara tabbatar mana cewa muna rayuwa a lokacin da Littafi Mai Tsarki ya kira, “kwanakin karshe.” (2 Timoti 3:1) Kwanakin karshen sun soma a shekara ta 1914. Ga wasu abubuwan da suka yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya fada za su faru a zamaninmu:

 “Yake-yake.”Matiyu 24:6.

  •   “A Shekara Ta 2022 Ce Aka Sake Soma Yaki a Turai.” a

 Ka duba talifin nan, “Rasha ta Kai wa Yukiren Hari.”

 “Yunwa.”Matiyu 24:7.

  •   “2022: Shekarar da Aka Yi Fama da Yunwa da Ba a Taba Yi Ba.” b

 “Annoba.”Luka 21:11, Littafi Mai Tsarki.

  •   “Cutar polio ta sake dawowa, cutar kyanda ko monkeypox kuma ta zama babbar matsala. Kari ga haka, annobar korona ta ci gaba da yin barna. Wannan yanayin ya nuna yadda cuttuttuka masu yaduwa da wuri suke da lahani ga lafiyar ꞌyan Adam.” c

 “Abubuwa masu ban tsoro.”Luka 21:11.

  •   “An yi zafi mai tsananin da ba a taba yi ba, da fari da gobaran daji, da kuma ambaliya. Ba za a taba mantawa da shekarar 2022 ba, wanda aka yi balaꞌoꞌi iri-iri da suka jawo barna sosai kuma sun halaka mutane da yawa a fadin duniya.” d

 Ka duba talifin nan, “Tsananin Zafi da Ake Yi A Fadin Duniya.”

 “Tashin hankali.”Luka 21:9.

  •   “Fadiwar tattalin arziki da tsadan kayayyaki sun sa mutane fushi sosai don haka, an yi zanga-zanga kin jinin gwamnati sosai a 2022.” e

Me zai faru a shekara mai zuwa?

 Babu wani a cikinmu da zai iya fadan abin da zai faru a shekara ta 2023. Abin da muka sani shi ne, nan ba da dadewa ba, Mulkin Allah zai kawo canji a duniya. (Daniyel 2:44) Mulkin zai kawar da duk abubuwan da ke jawo matsaloli a duniya kuma ya sa a yi nufin Allah.—Matiyu 6:9, 10.

 Muna karfafa ka ka bi shawarar da Yesu ya bayar cewa, “ku zauna da shiri” don ku ga yadda abubuwan da ke faruwa a duniya suke cika annabcin da ke Littafi Mai Tsarki. (Markus 13:37) Don samun karin bayani game da yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka yanzu, da kuma yadda kai da iyalinka za ku kasance da bege, ka tuntube mu.

a AP News, “2022 Was Year the Horror of War Returned to Europe,” wanda Jill Lawless ya wallafa a ranar 8 ga Disamba, 2022.

b Kungiyar WFP (World Food Programme), “A Global Food Crises.”

c JAMA Health Forum, “Living in an Age of Pandemics—From COVID-19 to Monkeypox, Polio, and Disease X,” wanda Lawrence O. Gostin, JD, ya wallafa a 22 ga Satumba, 2022.

d Earth.Org, “What’s Behind the Record-Breaking Extreme Weather Events of Summer 2022?” wanda Martina Igini, ya wallafa a 24 ga Oktoba, 2022.

e Carnegie Endowment for International Peace, “Economic Anger Dominated Global Protests in 2022,” wanda Thomas Carothers da Benjamin Feldman, suka wallafa a 8 ga Disamba, 2022.