Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Photo by Zhai Yujia/China News Service/VCG via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Ambaliyar Ruwa Masu Barna​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Ambaliyar Ruwa Masu Barna​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 A duk fadin duniya, mutane da yawa suna fama da barnar da ambaliyar ruwa ke jawowa. Ga wasu rahotanni:

  •   A labaran AP na 2 ga Agusta, 2023, an ce: “A kwanan nan, an tafka ruwan sama sosai fiye da wanda aka taba yi cikin shekara 140 da suka shige a birnin tarayyar China. Ruwan saman ya kai . . . inci 29.3 a tsakanin ran Asabar da Laraba.”

  •   A ran 3 ga Agusta, 2023, kafar yada labarai na Deutsche Welle ya ce: “Mahaukaciyar guguwa da ake kira Khanun ne ta sa aka sake tafka ruwan sama da iska mai karfin gaske a kudancin Japan a ran Alhamis, har mutane biyu sun mutu. . . . Ana tsammanin cewa ruwan saman zai kai kafa 2 a Taiwan ta tsakiya da ke kan tudu.”

  •   A labaran BBC na 24 ga Yuli, 2023, an ce: “Ambaliyar da aka yi [a Nova Scotia] a karshen mako, ya faru ne don ruwan sama mai tsanani da aka yi a Atlantic a yankin Kanada a cikin shekarar 50 da suke shige.”

 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da abubuwan nan?

Alamar “kwanakin karshe”

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna rayuwa ne a lokacin da ake kira “kwanakin karshe.” (2 Timoti 3:1) Yesu ya yi annabci cewa a zamanin nan, za mu ga “abubuwa masu ban tsoro.” (Luka 21:11) Canjin yanayi yana cikin abubuwan da suka sa muke ganin yanayoyi masu ban tsoro ba zato ba tsammani. Abubuwan nan suna yawan faruwa yanzu kuma suna dada muni.

Abin da ya muke da bege

 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ya kamata abubuwan ban tsoro da suke faruwa a yau su sa mu kasance da bege. Me ya sa? Yesu ya ce: “Idan kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani Mulkin Allah ya yi kusa.”​—Luka 21:31; Matiyu 24:3.

 Abubuwan da suke faruwa yanzu sun nuna cewa Mulkin Allah ya kusa ya kawo karshen balaꞌoꞌin da suke faruwa a duniya har da ambaliya masu barna.​—Ayuba 36:​27, 28; Zabura 107:29.

 Don ka ga yadda Mulkin Allah zai maida duniyar nan yadda take a dā, ka duba talifin nan “Who Will Save the Earth?