Bayanin da Ke Baibul Game da Zaman Yahudawa a Babila Gaskiya Ne?
Shekaru 2,600 da suka shige, Babiloniyawa sun kwashe Yahudawa zuwa bauta a Babila, kuma sun yi kusan shekaru 70 a wurin. Allah ya annabta irin rayuwar da Yahudawa da aka kai bauta a Babila za su yi, ya ce: “Ku gina wa kanku gidaje ku zauna a ciki. Ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu. Ku auri mata, ku haifi ’ya’ya maza da mata. . . . Amma ku nemi zaman lafiyar wurin da na kai ku bauta.” (Irmiya 29:1, 4-7) Amma Yahudawan sun yi irin wannan rayuwar kuwa?
Masu bincike sun yi nazari akan alluna sama da 100 da aka samo daga Babila ta dā. Allunan sun nuna cewa yawancin Yahudawan ba su daina bin al’adu da addininsu ba, kuma sun yi iya kokarin bin dokokin Babiloniyawa. An rubuta allunan a shekara ta 572 zuwa 477 K.Z., allunan suna dauke da wata yarjejeniya da ayyukan kasuwanci da wata rubutaccen alkawari da kuma bayanan harkokin kudi. “Wani bincike ya ce, wadannan rubutun “sun bayyana irin rayuwar da mutanen da suke bautar suka, suna noma kuma sun gina gidaje, suna biyan haraji da kuma yin aiki wa tsarki.”
Wannan rubutun ya nuna cewa Yahudawa da yawa sun zauna a wani gari da ake kira Al-Yahudu, ko kuma garin Yahuda. An rubuta sunayen zamanai hudu na Yahudawa a jikin allon da harshen Yahudanci aka rubuta wasu cikinsu. Kafin a samo allon, abu kadan ne kawai masanan ilimi suka sani game da irin rayuwar da Yahudawa suka yi a Babila. Dr. Filip Vukosavovic, daya ne daga cikin darektoci da ke Kula da Kayan Tarihi a Isra’ila ya ce: “Ta wurin allon nan ne muka kara koya game da Yahudawan, ta hakan ne muka san sunayensu, inda suka yi zama, da lokacin da suka yi zaman, da kuma irin rayuwar da suka yi.”
Yahudawan suna da ’yancin yin abin da suke so lokacin da suke zaman bauta. Vukosavovic ya ce “ba a Al-Yahudu kadai suka zauna ba amma sun zauna a wasu garuruwa ma.” Wadansu a cikinsu sun koya aikin hanu dabam-dabam, wanda daga baya ya taimaka masu a gina Urushalima. Allunan Al-Yahudu sun kuma nuna cewa wadansu Yahudawan sun ci gaba da zama a Babila bayan sun gama zaman bautarsu. Wannan ya nuna cewa sun ji dadin zamansu a Babila, kamar yadda Kalmar Allah ya annabta.