Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Comstock Images/Stockbyte via Getty Images

WAꞌAZI NA MUSAMMAN

ꞌYan Siyasa Masu Cin Hanci da Rashawa​—Abin da Mulkin Allah Zai yi

ꞌYan Siyasa Masu Cin Hanci da Rashawa​—Abin da Mulkin Allah Zai yi

 Mutane suna neman shugabannin gwamnatin da za su iya amince da su domin su gaji da ꞌyan siyasa masu cin hanci da rashawa. A wani bincike da aka yi a duk fadin duniya a shekara ta 2023 an gano cewa rukunin mutane da aka fi nuna musu rashin yarda su ne shugabannin gwamnatin. a

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai gwanmati wanda shugabansa na da aminci da gaskiya kuma ba ya cin hanci da rashawa. Gwamnatin Mulkin Allah ne kuma Shugaban mulkin Allah Yesu Kristi ne.​—Ishaya 9:7.

 Yesu ya riga ya nuna ta ayyukansa yadda ya damu da mutane. (Matiyu 9:​35, 36) A matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah zai sa wadanda suka amince da mulkinsa su sami adalci da salama.​—Zabura 72:​12-14

a Rahoton Kungiyar Edelman Trust Barometer Global na 2023.