KU ZAUNA A SHIRYE!
Sanannen Maꞌaikacin Kiwon Lafiya Ya Ce Dandalin Sada Zumunta Zai Iya Kasance da Mugun Sakamako ga Matasa—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
A ranar 23 ga Mayu, wani sanannen maꞌaikacin kiwon lafiya a Amirka ya yi kashedi cewa dandalin sada zumunta yana shafan matasa da yawa.
Wata kungiyar ba da shawara da ake kira Social Media and Youth Mental Health: The U.S. Surgeon General’s Advisory, 2023 ta ce: “Dandalin sada zumunta yana amfanar wasu yara da matasa. Amma da akwai tabbaci cewa zai iya kasance da lahani sosai ga lafiyar jiki da na kwakwalwar yara da matasa.”
Kungiyar ta ba da rahoton da ya nuna dalilin da ya sa ya kamata mu damu.
Yara ꞌyan shekara 12 zuwa 15 da suke “yin fiye da saꞌoꞌi 3 kowace rana a dandalin sada zumunta za su samu matsalar kwakwalwa. Hakan ya kunshi tsananin bakin ciki da damuwa.”
Yara ꞌyan shekara 14, “da suke yin amfani da dandalin sada zumunta suna fama da rashin barci. Akan zarge su a dandalin kuma ba sa so siffarsu. Kari ga haka, sukan ji ba su da amfani kuma suna tsananin bakin ciki. An nuna cewa wadannan abubuwa sun fi damun ꞌyammata a kan maza.”
Ta yaya iyaye za su iya kāre yaransu daga wadannan hadaruruka? Akwai shawarwarin da za su taimaka a Littafi Mai Tsarki.
Abin da iyaye za su iya yi
Ku dauki mataki. A matsayinku na iyaye, ku yi tunani game da hadaruruka da ke tattare da dandalin sada zumunta kuma ku tsai da shawara ko yaranku za su yi amfani da shi ko aꞌa.
Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Koyar da ꞌyaꞌyanka cikin hanyar da za su bi.”—Karin Magana 22:6.
Don samun karin bayani, ku karanta talifin nan “Should My Child Use Social Media?”
Idan ka bar yaronka ya yi amfani da dandalin sada zumunta, ka san abubuwa da za su iya jawo masa lahani kuma ka rika lura da abubuwan da yake yi a dandalin. Ta yaya za ku yi hakan?
Ka kāre yaronka daga abubuwa masu lahani a dandalin sada zumunta. Ka koya wa yaronka ya san abubuwan da za su jawo masa matsala a dandalin kuma ya guje su.
Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Kada ma a ko ambaci iskanci da kowane irin aikin lalata ko kwadayi a tsakaninku, . . . Haka ma da kazamar magana da zancen banza da wawanci, gama ba su dace da ku ba. A maimakon haka ku dinga gode wa Allah.”—Afisawa 5:3, 4.
Don samun shawarwari, ku karanta talifin nan “Teaching Your Teenager Social Media Safety.”
Ku kafa iyaka. Alal misali, ku kafa dokoki a kan tsawon lokaci da yaranku za su yi amfani da dandalin sada zumunta.
Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Ku mai da hankali kwarai ga zamanku. . . . Ku zama kamar . . . masu hikima. Ku yi amfani da kowane zarafi na yin kirki.”—Afisawa 5:15, 16.
Ku yi amfani da bidiyon zanen allo Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta na Intane don ku taimaka wa yaranku su fahimci dalilin da ya sa kafa yawan lokaci da za su rika yi a dandali ya dace.