Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Tsananin Zafi da Ake Yi A Fadin Duniya​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Tsananin Zafi da Ake Yi A Fadin Duniya​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 A watan Yuli 2022, an yi matsanancin zafi a fadin duniya:

  •   A ranar 25 ga Yuli, 2022, CNN Wire Service ta ba da rahoto cewa: “A karo na biyu a wannan watan, hukumomi a kasar Caina sun sanar cewa za a yi matsanancin zafi a kusan birane 70.”

  •   A ranar 17 ga Yuli, 2022, jaridar The Guardian ta ba da rahoto cewa: “Yawan zafin da ake yi a Turai ya sa ana gobarar daji a kasashe da yawa.”

  •   A ranar Lahadi 24 ga Yuli, 2022, jaridar The New York Times ta ce: “An yi matsanancin zafi da ba a taba yin irinta ba a wasu birane a Amirka.”

 Mene ne dukan wadannan abubuwan suke nufi? Shin hakan yana nufin za a kai lokacin da ba za a iya rayuwa a duniya ba? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

An yi annabci game da tsananin zafi a Littafi Mai Tsarki ne?

 E. Tsananin zafi ya jitu da abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a wannan lokacin. Alal misali, Yesu ya yi annabci cewa za mu ga “abubuwa masu ban tsoro da alamu masu ban mamaki.” (Luka 21:11) Matsanancin zafi da ake yi a fadin duniya ya sa mutane da yawa suna ganin cewa za a kai lokacin da ba za a iya rayuwa a duniya ba.

Shin za a kai lokacin da ba za a iya rayuwa a duniya ba?

 Aꞌa. Allah ya yi duniya don ꞌyan Adam su yi rayuwa a cikinta har abada. (Zabura 115:16; Mai-Waꞌazi 1:4) Ba zai bar ꞌyan Adam su halaka duniya ba. Maimakon haka, ya yi alkawari cewa zai “halaka masu halaka duniya!”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18.

 Bari mu tattauna annabci guda biyu da suka nuna wasu alkawura da Allah ya yi game da duniya:

  •   “Daji da busasshiyar kasa za su yi murna, hamada za ta yi farin ciki ta fitar da fulawa ta ba da amfani.” (Ishaya 35:1) Allah ba zai bar duniya ta zama wuri da ba za a iya rayuwa a cikinta ba. Maimakon haka, zai gyara wuraren da suka lalace.

  •   “Kana kula da kasa ta wurin ba da ruwan sama, ka sa ta ba da amfani mai yawa.” (Zabura 65:9) Allah zai sa duniya ta zama aljanna.

 Don karin bayani game da yadda sauyin yanayin duniya take cikan annabcin Littafi Mai Tsarki, ka karanta talifin nan “Climate Change and Our Future​—What the Bible Says.”

 Don karin bayani game da alkawari da ke Littafi Mai Tsarki cewa za a gyara duniya, ka karanta talifin nan “Who Will Save the Earth?”