Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Harbe-harbe da Ake Yi A Makarantu?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Harbe-harbe da Ake Yi A Makarantu?

 A ranar 24 ga Mayu, 2022, wani mummunan balaꞌi ya adabi wani karamin garin Uvalde a jihar Texas da ke Amirka. Jaridar The New York Times, ta ce “wani dan bindiga ya kashe yara goma sha tara da malamai biyu . . . a makarantar firamare da ake kiran Robb Elementary School.”

 Abin bakin ciki shi ne, irin wadannan abubuwan masu ban tsoro sun zama ruwan dare gama gari. Jaridar USA Today ta ce a Amirka kadai, “an yi harbe-harbe 249 a makarantu a shekarar da ta shige. Wannan ce shekarar da aka fi yin harbe-harbe tun shekarar 1970.”

 Me ya sa wadannan mummunan abubuwa suke faruwa? Ta yaya za mu iya jimre da irin wadannan balaꞌoꞌin? Muna da bege cewa za a daina mugunta kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar.

Me ya sa ake dada mugunta a duniya?

  •    Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lokacin da muke ciki “kwanakin karshe,” lokacin da mutane da yawa za su zama “marasa kauna” da kuma “marasa tausayi,” suna yin munanan abubuwa. Abubuwan da mutane da suke nuna irin wadannan halayen suke yi “zai yi ta kara muni.” (2 Timoti 3:​1-5, 13) Don ku sami karin bayani, ku karanta talifin nan “Did the Bible Predict the Way People Think and Act Today?”

 Mutane da yawa sukan yi tunani cewa, ‘Me ya sa Allah ba ya hana irin wannan mummunan balaꞌi kamar harbe-harbe a makarantu?’ Don ku sami amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da, ku karanta talifin nan “Don Me Masifu Suke Fada wa Mutanen Kirki?

Ta yaya za mu iya jimre da irin wannan balaꞌin?

  •    “Abin da aka rubuta tun dā a cikin Rubutacciyar Maganar Allah an rubuta ne domin a koyar da mu, domin mu zama da sa zuciya . . . da karfafawa wadanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.”​—Romawa 15:4.

 Kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu jimre da wannan muguwar duniya. Ka duba mujallar Awake! mai jigo “Will Violence Ever End?” don ku sami karin bayani.

 Don samun shawarwarin a kan yadda iyaye za su iya taimaka wa yaransu su jimre da labarai masu ban tsoro, ku karanta talifin nan “Ku Taimaki Yaranku Su Rage Damuwa a kan Labarai Masu Ta Da Hankali.

Za a daina mugunta kuwa?

  •    “Daga masu danniya da masu tā da hankali yakan fanshe su.”​—Zabura 72:14.

  •    “Za su mai da takubansu garmar noma, māsunsu kuma wukaken gyara itatuwa. Alꞌumma ba za ta kara daga takobin yaki da wata alꞌumma ba. Ba za su kara koyon dabarar yaki kuma ba.”​—Mika 4:3.

 Allah zai yi abin da ꞌyan Adam ba su iya yi ba. Mulkinsa zai kawar da dukan makamai kuma ya kawo karshen mugunta. Don ku kara koya game da abin da Mulkin Allah zai cim ma, ku karanta talifin nan “Under God’s Kingdom ‘Peace Will Abound.’”