Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Justin Paget/​Stone via Getty Images

Ta Yaya Za Ka Iya Jimre da Kadaici da Ya Zama Matsala a Duniya??

Ta Yaya Za Ka Iya Jimre da Kadaici da Ya Zama Matsala a Duniya??
  •   Bayanai daga Our Epidemic of Loneliness and Isolation: The U.S. Surgeon General’s Advisory on the Healing Effects of Social Connection and Community, 2023 sun ce: “Kusan rabin mutanen Amirka sun ce sun kadaita, kuma matasa ne suka fi fama da hakan.”

  •   A rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da a ranar 15 ga Nuwamba, 2023, an ce: “[Hukumar Lafiya ta Duniya] ta sanar cewa ta ba wani rukuni aikin yin bincike da kuma bi da kadaici a matsayin ciwo na gaggawa. Rukunin za su karfafa wadanda suka kadaita su mai da hankali wajen kulla abokantaka da mutane. Ban da haka, za a nemi hanyoyi kawar da kadaici a dukan kasashe, ko da kasashen talakawa ne suka fi yawa.”

 Littafi Mai Tsarki na dauke da shawarwari da za su taimaka wa mutane su nemi abokai na kwarai da zai sa ba za su kadaita ba.

Kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka

 Ka rage ayyuka da suke hana ka yin cudanya da mutane. Irin wadannan ayyuka sun kunshi yawan yin amfani da dandalin sada zumunta. Maimakon haka, ka nemi abubuwan da za su sa ka yi maꞌamala da mutane kuma ta hakan ka sami abokan kirki.

  •   Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “A koyaushe aboki yana nuna kauna, an haifi danꞌuwa kuwa domin taimako a kwanakin masifa.”​—Karin Magana 17:17.

 Ka nemi damar taimaka wa mutane: Idan muka yi wa mutane alheri, hakan zai karfafa abokantakarmu da su kuma zai sa mu farin ciki.

  •   Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Ya fi albarka a bayar da a karba.”​—Ayyukan Manzanni 20:35.

 Ka bincika dandalinmu don ka samu karin bayani daga Littafi Mai Tsarki game da yadda za ka kulla abota.