Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Yadda Kayayyaki Suke Kara Tsada?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Yadda Kayayyaki Suke Kara Tsada?

 A wani rahoto da shugaban Kungiyar Bankin Duniya ya bayar a watan Yuni 2022, ya ce, “tattalin arziki na duniya ya tabbarbare sosai. A wannan karon, farashin kayayyaki da hidimomi suna karuwa sosai kuma mutane ba su da isashen kudin kushewa.”

 International Monetary Fund sun ce: “Farashin man fetur da abinci sun karu sosai, kuma hakan ya shafi mutanen da ke kasashen da ke fama da talauci sosai.”

 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa muke fama da matsalar tattalin arziki, da yadda za mu iya jimrewa da kuma begen da muke da shi cewa za a kawar da wannan matsala gabaki daya.

Karuwan tsadan kayayyaki a “kwanakin karshe”

  •   Littafi Mai Tsarki ya kira lokacin da muke ciki “kwanakin karshe.”​—2 Timoti 3:1.

  •   Yesu ya ce “abubuwa masu ban tsoro” za su faru a wannan lokacin. (Luka 21:11) Mutane sukan ji tsoro saꞌad da farashin kayayyaki suna dada karuwa. Suna damuwa game da abin da zai faru a nan gaba da kuma yadda za su iya biya bukatun iyalansu.

  •   Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna ya annabta cewa farashin abinci zai karu a wannan lokacin. Ya ce: “Sai na ji wani abu mai kama da murya . . . tana cewa, ‘Mudun hatsin alkama na yawan kudin da lebura zai samu na aiki yini daya.’”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:6.

 Don ku kara koya game da “kwanakin karshe” da annabcin da ke littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, ku kalli bidiyon nan Duniya Ta Canja Sosai Tun Daga 1914 kuma ku karanta talifin nan “Su Wane ne Mahaya Hudun?

Yadda za a magance matsalar tattalin arziki

  •   “A kwanakin nan, mutane za su gina gidaje, su zauna a cikinsu, za su shuka gonakin inabi, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna a ciki ba, ba za su shuka gonaki, wani ya ci amfanin ba.”​—Ishaya 65:​21, 22.

  •   “Bari a sami hatsi a yalwace a kasar, a sa amfanin gona ya rufe kan tuddai.”​—Zabura 72:16.

  •   “Yahweh ya ce, ‘Tsanantawar matalauta, na gani, nishi mai zafi na masu bukata, na ji. To, yanzu zan tashi zan kiyaye su bisa ga bukatarsu!’”​—Zabura 12:5. a

 Nan ba da dadewa ba, Allah zai kawo karshen matsalar tattalin arziki a duniya gaba daya, ba a kasa guda daya kawai ba. Don ka ga yadda zai yi hakan, ka karanta talifin nan “Is a Fair Economic System Possible?”

 A yau ma, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka san yadda za ka jimre da karuwan farashin abubuwa. Ta yaya? Ya ba da shawarwari masu kyau a kan yadda za mu kasance da basira wajen kashe kudi. (Karin Magana 23:​4, 5; Mai-Waꞌazi 7:12) Don samun karin bayani, ka karanta talifofin nan “Protect Your Livelihood” da kuma “Yadda Za Ka Yi Manejin Kudin da Kake Samu.”

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.