Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

fcafotodigital/E+ via Getty Images

Wadanda Ba Sa Cin Nama​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Wadanda Ba Sa Cin Nama​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Mutane da yawa a fadin duniya sun zabi su ki cin nama.

  •   Kungiyar The Vegan Society ta ce: “Wadanda suke da raꞌayin nan suna iya kokarinsu su guji cutar da dabbobi, ko su yi amfani da su a matsayin abinci, ko kuma su yi amfani da fatarsu su yi riguna, da dai sauransu.”

 Wasu mutane suna kin cin nama ba don sun damu da dabbobi kawai ba, amma suna so su kyautata mahalli ko lafiyar jikinsu ko kuma saboda addininsu.

  •   Cibiyar Britannica Academic ta ce: “Mutane da suke kin cin nama suna da raꞌayin da ya bambanta da sauran mutane, domin suna ganin cewa zabin da suka yi ne zai sa duniya ta gyaru.”

 Shin kin cin nama ne zai sa duniya ta gyaru? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

Yadda Mahaliccinmu yake ganin ꞌyan Adam da dabbobi

 Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa Mahaliccinmu wato Jehobah Allah a yana daukan ꞌyan Adam fiye da dabbobi kuma ya ba mu iko a kan su. (Farawa 1:​27, 28) Daga baya Allah ya bar ꞌyan Adam su ci naman dabbobi a matsayin abinci. (Farawa 9:3) Amma, ba ya so ꞌyan Adam su ci zalin dabbobi.​—Karin Magana 12:10.

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kowa na da ꞌyanci ya zaba ko zai ci nama ko aꞌa. b Amma ba zabinmu ba ne zai sa mu zama da daraja a idon Allah ba. (1 Korintiyawa 8:8) Bai kamata mu kushe zabin da wasu suka yi gama da abin da za su ci ba.​—Romawa 14:3.

Abin da zai sa duniya ta gyaru

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba zabinmu ba ne zai sa duniya ta gyaru. Siyasa da tattalin arziki na duniyar nan, su ne suke jawo matsaloli da yawa, kuma babu wanda zai iya magance su. Littafi Mai Tsarki ya ce:

  •   “Duk abin da ya tankware ba a iya mikewa.”​—Mai-Wa’azi 1:15.

 Mahaliccinmu zai magance matsalolin da muke fama da su a yau. Littafi Mai Tsarki ya bayana yadda zai yi hakan.

  •   “Saꞌan nan na ga sabon sama da sabuwar kasa. Sama na farko da kasa ta farko duk sun bace, babu kuma teku.”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:1.

 Allah zai halaka gwamnatocin ꞌyan Adam ko kuma “sama na farko,” kuma ya kafa “sabon sama,” wato Mulkinsa. Mulkinsa zai cire “kasa ta farko” wato mugaye, sai ya yi sarauta a kan “sabuwar kasa,” wato wadanda suke a shirye su bi ja-gorancinsa.

 A karkashin Mulkin Allah ne kadai ꞌyan Adam za su koya yadda za su zauna lafiya da dabbobi kuma su daraja mahalli.​—Ishaya 11:​6-9.

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.

b Littafi Mai Tsarki ya ba da doka cewa “ku kiyaye kanku daga . . . jini.” (Ayyukan Manzanni 15:​28, 29) Hakan na nufin cewa ba za mu sha jini ba, ko mu ci mushe ko kuma mu ci abinci da aka saka jini a ciki.