Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Mutane Miliyan Shida Sun Mutu Sanadiyyar Cutar Korona​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mutane Miliyan Shida Sun Mutu Sanadiyyar Cutar Korona​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, a ran 23 ga Mayu, 2022, an gano cewa mutane miliyan 6.27 sun mutu sanadiyyar cutar korona. Amma, a wani labari da aka wallafa a ranar 5 ga Mayu, 2022, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutane da suka mutu sun fi hakan sosai. A shekara ta 2020 da 2021 hukumar ta ce: “Mutane da suka mutu sakamakon cutar korona ko kuma wasu cututtuka da ke da alaka da cutar sun kai miliyan 14.9.” Shin, akwai abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da irin wadannan balaꞌin?

An yi annabci a Littafi Mai Tsarki game da munanan annoba

  •    Yesu ya yi annabci cewa za a yi “Annoba” na munanan cututtuka a lokacin da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanakin karshe.”​—Luka 21:​11, Littafi Mai Tsarki; 2 Timoti 3:1.

 Annabcin da Yesu ya yi yana cika a yau. Don samu karin bayani, ka karanta talifin nan, “Mene ne Ake Nufi da Alamun ‘Kwanaki na Karshe’ ko ‘Karshen Duniya’?

Littafi Mai Tsarki yana karfafa mu

  •    “Allah wanda yake yi mana . . . ta’aziyya! Yana yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalarmu.”​—2 Korintiyawa 1:​3, 4.

 Mutane da yawa da wani nasu ya mutu sun sami ta’aziyya daga Littafi Mai Tsarki. Don samun karin bayanai, ka karanta talifofin nan, “Coping With Grief​—What You Can Do Today” da kuma “The Best Help for Those Who Grieve.”

Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda za a magance matsalar

  •    “Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama.”​—Matiyu 6:10.

 Nan ba da dadewa ba, “Mulkin Allah” zai yi abin da zai sa “ba mazaunin kasar da zai ce: ‘Ina ciwo.’ ” (Markus 1:​14, 15; Ishaya 33:24) Don ka koyi game da gwamnatin da za a kafa a sama da kuma abin da za ta yi, ka kalli bidiyon nan Mene ne Mulkin Allah?

 Don kai da iyalinka ku amfana daga shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma alkawuran da Allah ya yi, ka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki.