Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sean Gladwell/Moment via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Kudin da Aka Kashe A Fadin Duniya a Kan Sojoji da Makamai Ya Wuce Dala Tiriliyan Biyu​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce??

Kudin da Aka Kashe A Fadin Duniya a Kan Sojoji da Makamai Ya Wuce Dala Tiriliyan Biyu​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce??

 A fadin duniya an kashe dalolin tiriliyan biyu da biliyan 24 a kan sojoji da makamai a shekara ta 2022, musmman domin hari da Rasha take kai wa Yukiren. Wannan ne kudi mafi yawa da aka taba kashewa. A wani rahoto da kungiyar Stockholm International Peace Research Institute (SIPRI) ta ba da a shekara ta 2022, ta ce:

  •   Kudin da aka kashe a Turai a kan sojoji da makamai ya karu da kashi 13 bisa dari a shekara ta 2022, kuma wannan ne kudin da gwamnatocin Turai suka fi kashewa tun shekara ta 1991.”

  •   “Rasha ta kara kudin da take kashewa da kashi 9.2 bisa dari, wannan ya sa ta zama kasa ta uku da ta fi kashe kudi a kan sojoji da makamai a duniya.”

  •   Amirka ce ta fi kashe kudi don tana kashe-kashe 39 bisa dari na kudin da ake kashewa a kan sojoji da makamai a fadin duniya.”

 Wani da ke cikin wadanda suka kafa kungiyar Stockholm International Peace Research Institute mai suna Dokta Nan Tian ya ce: “Da yake gwammnatoci sun ci gaba da kara kudin da suke kashewa a kan sojoji da makamai, hakan ya nuna cewa muna rayuwa a duniya da babu tsaro.”

 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa gwammnatoci mafi iko za su ci gaba da fada da juna, kuma ya gaya mana abin da zai kawo zaman lafiya na gaske a duniya.

An annabta cewa yake-yake za su karu

  •   Littafi Mai Tsarki ya kira lokacin da muke ciki “kwanakin karshe.”​—Daniyel 8:19.

  •   Littafin Daniyel ya annabta cewa a lokacin, za a samu gwamnatoci da za su rika gasa da juna. Wadannan gwamnatocin za su rika ja da juna don neman zama mafi iko. A garin yin hakan, za su rika kashe “dukiya” ko kuma kudade masu yawan gaske.​—Daniyel 11:​40, 42, 43.

 Don samun karin bayani game da wannan annabcin Littafi Mai Tsarki mai kayatarwa, ka kalli bidiyon nan Annabcin da Ya Cika​—Daniyel Sura 11.

Yadda za a samu zaman lafiya na gaske

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai kawar da gwamnatoci na ꞌyan Adam. Zai “kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a ba wadansu su gāje shi ba. Mulkin nan zai farfashe dukan wadannan mulkokin, ya kawo karshensu. Amma mulkin nan zai kasance har abada.”​—Daniyel 2:44.

  •   Ba da dadewa ba, Jehobah a zai yi abin da ya gagari ꞌyan Adam, zai sa mu rika zaman lafiya har abada. Ta yaya zai yi hakan? Mulkinsa zai kawar da dukan makamai kuma ya kawo karshen dukan mugunta.​—Zabura 46:​8, 9.

 Don samun karin bayani game da abin da Mulkin Allah zai yi, ka karanta talifin nan “Under God’s Kingdom ‘Peace Will Abound.’

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.