Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Maka Ka Daina Shan Kwaya?

Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Maka Ka Daina Shan Kwaya?

 Kowace shekara, miliyoyin mutane suna mutuwa sakamakon abubuwan da suke sha, hakan ya hada da miyagun kwayoyi. A lokacin da ake annobar korona, wannan matsalar ta karu. Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mutane da yawa su daina shan kwaya. Idan kana fama da jarabar shan kwaya, Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka. a

A wannan talifin za ka ga

 Me ya sa zai dace mu nemi taimako daga Littafi Mai Tsarki?

 Masu bincike sun gano cewa mutane sukan soma shan miyagun kwayoyi ne don sun kadaita ko suna cikin damuwa ko kuma suna yawan tunani. Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka san yadda za ka shawo kan abubuwan da suke iya sa mutum cikin jarabar shan kwaya. Zai koya maka yadda za ka zama aminin Allah. (Zabura 25:14) Da taimakon Allah, za ka iya shawo kan matsalolin da kake ganin ba za ka iya magance su da kanka ba.​—Markus 11:​22-24.

 Matakai hudu daga Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa mutum ya daina shan kwaya

  1.  1. Ka koyi abubuwa game da Jehobah. b (Yohanna 17:3) Shi ne Mahalicci da kuma Tushen iko marar iyaka. Ban da haka ma, shi Uba ne mai kauna. Yana so ka kulla dangantaka da shi kuma yana so ya taimake ka. (Ishaya 40:​29-31; Yakub 4:8) Ya yi alkawari cewa za ka more rayuwa a nan gaba idan ka bi kaꞌidodinsa kuma ka kaunace shi.​—Irmiya 29:11; Yohanna 3:16.

  2.  2. Ka nemi taimakon Jehobah. Ka roki Allah ya taimaka maka ka shawo kan shaye-shaye, don hakan zai sa ka zama “mai tsarki [ko mai tsabta], da kuma abin karɓa ga Allah.” (Romawa 12:1) Ta wajen ruhunsa mai tsarki, zai ba ka ‘iko’ fiye da yadda kake tsammani. (2 Korintiyawa 4:7; Luka 11:13) Ikon nan zai taimaka maka ka daina shan miyagun kwayoyi kuma ka koyi “sabon halin” da ke faranta wa Allah rai.​—Kolosiyawa 3:​9, 10.

  3.  3. Ka kasance da raꞌayin Allah. (Ishaya 55:9) Zai tamaka maka ka ‘sabunta tunaninka da hankalinka,’ wato ka canja tunaninka. Kuma hakan zai taimaka maka ka daina shaye-shaye. (Afisawa 4:23) Littafi Mai Tsarki na dauke da tunanin Allah, don haka zai dace ka dinga karanta shi a kai a kai. (Zabura 1:​1-3) Mutane da yawa sun amfana don an taimaka musu su fahimci abubuwan da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. (Ayyukan Manzanni 8:​30, 31) Shaidun Jehobah suna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta. Kuma muna gayyatar ka ka halarci taronmu, domin a wurin ne muke koyan abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki da yadda za mu bi koyarwar a rayuwarmu.

  4.  4. Ka zabi abokan kirki. Abokanka za su iya sa ya yi maka sauki ko wuya ka shawo kan shaye-shaye. (Karin Magana 13:20) Allah yana so ya taimaka maka ka kulla abota da mutanen da suke bauta masa, domin yin hakan zai sa ka amfana. (Zabura 119:63; Romawa 1:12) Ka zabi nishadi mai kyau, domin irin mutanen da muke kallo ko saurara ko kuma karanta game da su, za su iya shafan mu. Ka guji duk abin da zai sa ya yi maka wuya ka yi abin da yake da kyau.​—Zabura 101:3; Amos 5:14.

 Ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa mutum ya daina shan kwaya

 Zabura 27:10: “Ko da babana da mamata sun yashe ni, Yahweh zai lura da ni.”

 Wani mai suna Wilby daga kasar Haiti ya ce: “Ban san babana ba, kuma hakan ya sa na ji kamar rayuwata ba ta da maꞌana. Da na koya game da Jehobah kuma na san cewa yana kaunata, sai rayuwata ta kasance da maꞌana, kuma hakan ya sa na daina shaye-shaye.”

 Zabura 50:15: “Ku kira gare ni a lokacin wahala, zan kubutar da ku.”

 Wani mai suna Serhiy daga kasar Yukiren ya ce: “Ayar nan ta karfafa ni sosai in ci gaba da yin kokarin shawo kan matsalata, ko da na kasa yin hakan a wasu lokuta. Lalle Jehobah ya cika alkawarinsa.”

 Karin Magana 3:​5, 6: Dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka. A dukan hanyoyin rayuwarka ka girmama shi, shi kuwa zai daidaita hanyoyinka.”

 Wani mai suna Michele daga kasar Italiya ya ce: “Ayoyin nan sun taimaka mini kada in dogora ga kaina, amma in dogara ga Jehobah. Da taimakonsa na canja rayuwata gabaki daya.”

 Ishaya 41:10: “Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kada ka damu, gama ni ne Allahnka. Zan sa ka yi karfi, in kuma taimake ka, zan rike ka da hannun damana mai nasara.”

 Wani mai suna Andy, daga Afrika ta Kudu ya ce: “Idan ban sami damar shan kwaya ba, hakan yakan sa ni tsananin damuwa. Nassin nan ya tabbatar mini cewa Allah zai taimaka min in shawo kan damuwata, kuma Allah ya yi hakan.”

 1 Korintiyawa 15:33 “Kada fa a rude ku! “Zama da mugaye yakan bata halayen kirki.”

 Wani mai suna Isaac daga kasar Kenya ya ce: “Yin tarayya da abokan banza ne ya sa na soma shan kwaya. Amma na daina shan kwaya saꞌad da na daina yin cudanya da su, kuma na soma yin abokantaka da mutane da nake son salon rayuwarsu.”

 2 Korintiyawa 7:1: “Bari mu tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu ya kazantu.”

 Wata mai suna Rosa daga kasar Colombia ta ce: “Kalmomin nan sun karfafa ni in ci gaba da yin kokarin tsabtace jikina, kuma in daina shan kwaya da yin abubuwan da suke jawo mini illa.”

 Filibiyawa 4:13: “Zan iya yin kome ta wurin . . . wanda yake karfafa ni.”

 Wata mai suna Patrizia daga kasar Italiya ta ce: “Na san cewa ba zan iya daina shan kwaya da kaina ba, shi ya sa na yi adduꞌa Allah ya taimaka mini, kuma ya ba ni karfin da nake bukata.”

 Labaran mutanen da Littafi Mai Tsarki ya taimaka musu su daina shaye-shaye

 Joseph Ehrenbogen ya yi girma a inda ake tashin hankali sosai, hakan ya sa ya zama mashayin giya da taba da marijuana da kuma heroin. Sau da yawa ya kusan mutuwa don yawan abubuwan da yake sha. Akwai wani wuri a Littafi Mai Tsarki da ya tabbatar masa cewa zai iya canja halinsa. Ka karanta labarinsa a talifin nan “Na Koya Mutunta Kaina da Kuma Mata.”

 A wasu lokuta Dmitry Korshunov yakan koma shan kwaya da yake iya kokarinsa ya daina. Ka kalli bidiyo nan ‘Na Gaji da Salon Rayuwata’ don ka ga abin da ya taimaka masa ya yi nasara.

 Shin, Littafi Mai Tsarki ya hana zuwa asibiti neman taimako don shaye-shaye?

 Aꞌa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.” (Matiyu 9:12) Kungiyar National Institute on Drug Abuse ta ce: “Jarabar shan miyagun kwayoyin cuta ce mai tsanani, idan mutum yana so ya daina zai bukaci taimako sosai.” Hakika, taimakon Allah ne ya fi duk wani taimakon da mutumin zai yi wa kansa. Duk da haka, mutane da yawa da Littafi Mai Tsarki ya taimaka musu su daina shan kwayoyi su ma sun bukaci taimakon likita. c Alal misali wani mai suna Allen ya ce: “Lokacin da nake kokari in daina shan giya, sai duk jikina ya soma mini ciwo sosai.” A lokacin ne na gano cewa ba taimakon Littafi Mai Tsarki nake bukata kawai ba, amma wajibi ne in je in gan likita.”

 Littafi Mai Tsarki ya haramta shan magani ne?

 Aꞌa. A gaskiya Littafi Mai Tsarki ya nuna amfani ruwan inabi a matsayin magani, ko yin amfani da shi wajen rage zafin ciwon wanda yake bakin mutuwa. (Karin Magana 31:6; 1 Timoti 5:23) Kamar yadda yake da giya, yawan shan magani ciwon jiki zai iya zama mana jiki. Sabode haka ya kamata mu mai da hankali ga yadda muke shan maganin ciwon jiki.​—Karin Magana 22:3.

a Ko da yake a talifin nan an mai da hankali a kan yadda za a shawo kan miyagun kwayoyi, kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da aka tattauna za su iya taimaka ma wadanda suke fama da matsaloli kamar shan giya da taba da yawan cin abinci da buga caca da kallon batsa da kuma yawan amfani da dandalin sada zumunta.

b Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Ka karanta talifin nan “Wane ne Jehovah?

c Wuraren kiwon lafiya da asibitoci da kuma wasu shirye-shiryen da ake yi na ba da taimako za su iya taimaka wa mutum. Kowane mutum ne zai bincika sosai ya san irin jinyar da ta fi dacewa da shi.​—Karin Magana 14:15.