Kadaici, Matsala Ce da Ke Karuwa—Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce
Wani bincike da aka yi kwanan nan a wurare dabam-dabam a fadin duniya a ya nuna cewa, wajen mutum daya cikin hudu yana jin kadaici.
Chido Mpemba, wata mai kujera na sashen da ke kula da harkokin zaman jamaꞌa a Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce: “Mutum zai iya yin fama da kadaici komin shekarunsa da kuma wurin da yake zama.”
Wasu suna ganin cewa tsofaffi ko wadanda suke zama su kadai ne suke fama da kadaici. Amma matasa da masu koshin lafiya da masu arziki da wadanda suka yi aure ma suna iya fama da wannan matsalar. Rashin cudanya da mutane, da kuma jin kadaici zai iya shafan lafiyar mutum.
Wani likita a Amirka mai yin fida, mai suna Vivek Murthy ya ce: “Kadaici ya wuci jin bakin ciki.” Ya kara da cewa: “Hadarin mutuwa da ke tattare da rashin cudanya da mutane yana kamar hadarin mutuwa da ke tattare da shan karan sigari 15 a rana.”
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
Mahaliccinmu ba ya so mu ki yin cudanya da mutane. Nufin Allah ne mutane su more cudanya mai kyau da kuma gamsuwa.
Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Allah ya ce, . . . ‘Bai yi kyau mutumin ya kasance shi kadai ba.’ ”—Farawa 2:18.
Allah yana so mu kulla dangantaka da shi. Ya yi alkawari cewa idan muka yi kokari mu kusace shi, shi ma zai kusace mu.—Yakub 4:8.
Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Masu farin ciki ne wadanda suka san cewa suna bukatar kulla dangantaka da Allah, domin za su gāji mulkin sama.”—Matiyu 5:3, New World Translation.
Allah yana so mu bauta masa tare. Idan muka yi hakan za mu yi farin ciki sosai.
Kaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Mu lura da juna ta yadda za mu iza juna ga nuna kauna da yin aikin nagarta. Kada mu bar yin taron sujada. . . . A maimakon haka mu dinga ƙarfafa juna.”—Ibraniyawa 10:24, 25.
Don samun karin bayani a kan dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu guji kadaici, ka karanta talifin nan “Loneliness in a World of Mass Connection.”
a The Global State of Social Connections, by Meta and Gallup, 2023.