Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

E+/taseffski/via Getty Images (Stock photo. Posed by model.)

KU ZAUNA A SHIRYE!

Karuwar Matsalar Kwakwalwa Tsakanin Matasa​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Karuwar Matsalar Kwakwalwa Tsakanin Matasa​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 A ranar Litinin, 13 ga Fabrairu, 2023, hukumar CDC (Centers for Disease Control and Prevention) a Amirka ta fitar da rahoto game da matsalar kwakwalwa na matasa a Amirka. Ta ce wajen kashi 40 cikin 100 na daliban da suke sakandare suna fama da bakin ciki mai tsanani da kuma ji kamar ba su da amfani.

 Dr. Kathleen Ethier darektan hukumar CDC na bangaren hukumar DASH (Division of Adolescent and School Health) ya ce: “Ko da yake mun ga yadda matsalar take karuwa a tsakanin matasa a cikin shekaru 10 da suka shige, yawan ꞌyan matan da suke fama da matsalar kwakwalwa da tunanin kashe kansu da makamantansu ya karu sosai fiye da yadda muka taba gani.”

 A cikin rahoton an ce:

  •   Ana tilasta wa fiye da kashi 14 cikin 100 na matasa ma su yi jimaꞌi a lokacin da ba sa so su yi hakan. Dr. Ethier ya ce: “Wannan abin tsoro ne. Wato, a cikin kowane ꞌyan mata 10 da ka sani, ba mamaki an riga an yi wa 1 fyade.”

  •   Kusa 1 cikin ꞌyan mata 3 (wato kashi 30 cikin 100) sun taba tunanin yadda za su kashe kansu.

  •   Kusan 3 cikin ꞌyan mata 5 (wato kashi 57 cikin 100) suna fama da bakin ciki mai tsanani.

 Abubuwan nan da ake fada abin bakin ciki ne sosai. Ya kamata mutum a ya yi farin ciki a lokacin da yake matashi. Me zai taimaka wa matasa su san yadda za su bi da matsalolin da suke fuskanta? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun?

Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa matasa

 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda rayuwa za ta kasance da wuya a zamanin nan. Ya ce: “Za a sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:​1-5) Amma, Littafi Mai Tsarki na dauke da shawarwarin da za su iya taimaka wa miliyoyin matasa a fadin duniya su san yadda za su bi da matsalolinsu. Talifofi na gaba suna dauke da shawarwari daga Littafi Mai Tsarki.

 Taimako don matasan da suke fama da tunanin kashe kansu

 Taimakon don matasan da suke fama da bakin ciki mai tsanani, ko mugun tunani

 Taimakon don matasan da ake cin zalinsu

 Taimako don matasan da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata

Akwai shawarwarin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka wa iyaye

 Akwai shawarwarin da ke Littafi Mai tsarki da za su iya taimaka wa iyaye. Iyaye kuma su taimaka wa yaransu da suke fama da matsalolin rayuwa. Ga wasu talifofi da suke dauke da shawarwari daga Littafi Mai Tsarki.