Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TheCrimsonMonkey/E+ via Getty Images

WAꞌAZI NA MUSAMMAN

Matsalolin Mahalli—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Matsalolin Mahalli—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

 A ranar 25 ga Yuli, 2023, Inger Anderson, shugabar hukumar kare Mahalli ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce: “Yadda yanayi yake ta canjawa na jawo ma ꞌyan Adam da dabbobi da kuma itatuwa matsaloli. Hakan na dada muni domin guguwa tana halaka gidaje da kuma wuraren ayyuka a fadin duniya. Tekuna sun soma zama da dumi sosai kuma hakan zai iya sa dabbobi da tsire-tsire da yawa su mutu.”

 Shin gwamnatoci za su iya hada kansu su yi aiki tare don su magance matsalolin duniya? Za su iya kawo karshen matsaloli?

 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da wani gwamnatin da zai kawar da matsalolin Mahalli a duniya. Ya ce: “Allah na Sama zai kafa wani mulki,” wato gwamnatin da zai yi mulki bisa duniya kuma ya magance dukan matsaloli. (Daniyel 2:44) A lokacin “babu abin da zai cutar ko ya halaka” wani ko duniya.​—Ishaya 11:9.