Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kim Steele/The Image Bank via Getty Images

WAꞌAZI NA MUSAMMAN

Matsalolin Tattalin Arziki​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Matsalolin Tattalin Arziki​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

 A fadin duniya, yana yi wa mutane da yawa wuya su sami kudin biyan bukatunsu, kuma hakan na dada muni.

 Shin, shugabanni za su iya warware matsaloli gabaki daya ko kuma su dan inganta su?

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa akwai wata gwamnati da za ta magance dukan matsalolin tattalin arziki. Ya ce “Allah na Sama zai kafa wani mulki,” wato gwamnati guda daya da za ta kula da harkokin duniya. (Daniyel 2:44) A wannan gwamnatin, ba za a manta da kowa ba, ko a bar wani a baya ba. (Zabura 9:18) Mulkin Allah zai tabbatar da cewa kowa ya sami abin da yake bukata don ya more rayuwa. Kowa zai more albarkacin aikin hannuwansa.​—Ishaya 65:​21, 22.

a Rahoto na 2022-23 na kungiyar International Labour Organization Global Wage