KU ZAUNA A SHIRYE!
Me Ya Sa Siyasa Take Raba Kan Mutane Sosai?—Mene ne Littafi Mai Ya Ce?
A duk fadin duniya, kasashe da dama suna da raꞌayi dabam-dabam game da siyasa. A wani rahoto na 2022 da cibiyar Pew Research Centre mai nazarce-nazarce ta fitar, ya nuna cewa, “fiye da rabin mutane da aka tambaya a kasashe 19 sun ce yawan gardaman da ake samu a kasarsu tsakanin mutane suna faruwa ne domin mutane suna goyon bayan jam’iyyun siyasa dabam-dabam.”
Ka lura cewa siyasa tana dada raba kan mutane a yankinku? Me ya sa? Shin, akwai mafita? Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.
Halayen da ke rarraba mutane
Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa a zamaninmu da ake kira “kwanakin karshe,” mutane da yawa za su kasance da halayen da za su sa ya yi wuya a sami hadin kai.
“A kwanakin karshe za a sha wahala sosai. Gama mutane za su zama masu sonkansu, . . . [masu karya alkawari, New World Translation.]”—2 Timoti 3:1-3.
Duk da cewa mutane da yawa suna iya kokarinsu su ga cewa gwamnati ta yi nasara, hakan ba ya faruwa. Yana da wuya mutane da raꞌayinsu ya bambanta su yi aiki tare wajen magance matsaloli. Sakamakon da suke samu sun tabbatar da abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta tun a dā.
“Wadansu sukan sami mulki, wadansu kuwa su sha wuya a karkashinsu.”—Mai-Wa’azi 8:9, Littafi Mai Tsarki.
Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai mafita, wato gwamnatin da wanda yake shugabanci zai iya kawar da matsalolin da ke sa mutane shan wahala a yau.
Shugaban da ya damu da mu
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana wanda yake da iko ya magance matsalolin nan: wato Yesu Kristi. Yesu yana da iko ya sa a kasance da hadin kai da salama kuma yana marmari ya yi hakan.
“Bari adalci ya yalwata a kwanakinsa, salama ta karu.”—Zabura 72:7.
“Dukan alꞌummai kuma su yi masa hidima.”—Zabura 72:11.
Yesu shugaba ne da ya cancanta domin ya damu da mutane kuma yana so ya taimaka musu, musamman wadanda aka yi musu rashin adalci.
“Gama yakan kubutar da masu bukata yayin da suka yi kira, da matalauta da kuma marasa taimako. Yakan ji tausayin marasa karfi da masu bukata, yakan ceci rayukan matalauta. Daga masu danniya da masu tā da hankali yakan fanshe su.”—Zabura 72:12-14.
Ka dada koya game da Mulkin Allah wato gwamnatin da ke sama wanda Yesu ne sarki. Ka koyi yadda za ka amfana da yadda za ka goyi bayan mulkin.
Ka kalli bidiyon nan, Mene ne mulkin Allah?
Ka karanta talifin nan, “Mulkin Allah—Gwamnatin da Babu Cin Hanci da Rashawa.”