Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

mustafahacalaki/DigitalVision Vectors via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Kirkirarriyar Basira Ta AI Tana da Amfani Ne ko Lahani?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Kirkirarriyar Basira Ta AI Tana da Amfani Ne ko Lahani?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Kwanan nan, shugabanan duniya da masana kimiyya da masanan fasaha sun yi magana game da kirkirarriyar basira ta AI. Ko da yake sun ce tana da amfani sosai, amma sun damu da yadda mutane za su iya amfanin da ita a hanyar da ba ta dace ba.

  •   A ranar 4 ga Mayu, 2023, mataimakiyar shugaban kasar Amirka mai suna Kamala Harris ta ce: “Kirkirarriyar basira ta AI ne aka fi yin amfani da ita a yau, kuma tana inganta rayuwar mutane . . . Duk da haka, tana iya hana mu kasancewa da kwanciyar hankali, za ta iya dauke hakki ko sirrin ꞌyan Adam kuma ta sa ya yi mana wuya mu tabbata da yadda gwamnati ke sarauta.”

  •   A wani talifi da aka wallafa a ranar 9 ga Mayu, 2023, a littafin BMJ Global Health, a likitoci da masana kiwon lafiya a fadin duniya da Dokta Frederik Federspiel ne shugabansu sun ce: “Kirkirarriyar basira ta AI tana iya inganta yadda ake jinya a wasu hanyoyi, amma za ta iya jawo illa ga lafiyarmu a wasu hanyoyi.

  •   A ranar 1 ga Mayu, 2023, jaridar The New York Times, ta ce: “Mutane suna iya yin amfani da kirkirarriyar basira ta AI wajen yada karya. Nan ba da dadewa ba, mutane ba za su samu aikin yi ba. Wasu mutane da suke aikin fasaha sun damu sosai cewa a nan gaba kirkirarriyar basira ta AI za ta kasance da illa ga ꞌyan Adam.

 Da shigewar lokaci, za a sani ko mutane za su yi amfani da kirkirarriyar basira ta AI don su sa mutane su amfana ko kuma za su jawo musu lahani. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

Ta yaya kere-keren ꞌyan Adam yake jawo damuwa a cikin alꞌumma?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilin da ya sa ꞌyan Adam ba za su iya tabbatar cewa za a rika yin amfani da sabbin fasaha da suka kera don yin abubuwa masu kyau kawai ba.

  1.  1. Duk da cewa mutane suna son yin abin da zai amfani ꞌyan Adam, ba za su san cewa ayyukansu zai jawo mugun sakamako ba.

    •   “A ganin mutum, akwai hanyar da take daidai, amma ƙarshenta mutuwa ce.”​—Karin Magana 14:12.

  2.  2. Mutum ba zai iya sanin yadda mutane za su yi amfani da abin da kirkira ba, ko ta hanya mai kyau ko marar kyau.

    •   “Zan bar [aikina] wa wanda zai gāje ni. Wa ya sani ko shi wanda zai gāje ni mai hikima ne ko kuma wawa ne? Duk da haka, zai gāji dukan amfanin aikin da na sha wahalar tarawa a rayuwar duniyar nan.”​—Mai-Waꞌazi 2:​18, 19.

 Irin wannan rashin tabbaci ya nuna abin da ya sa muke bukatar ja-goranci daga Mahaliccinmu.

Ga wa za mu dogara?

 Mahaliccinmu ya yi alkawari cewa ba zai taba barin ꞌyan Adam ko kuma wani fasaha da mutane suka kera ya halaka duniya ko kuma ꞌyan Adam ba.

  •   “Duniya tana nan daram har abada.”​—Mai-Waꞌazi 1:4.

  •   “Masu adalci za su gāji kasar, su zauna a ciki har abada.”​—Zabura 37:29.

 A cikin Littafi Mai Tsarki, Mahaliccinmu ya gaya mana abin da za mu yi don mu yi rayuwar da za mu sami kwanciyar hankali a nan gaba. Don samun karin bayani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, ka karanta talifofin nan “A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?” da “A Real Hope for a Better Tomorrow.”

a Daga talifin nan “Threats by Artificial Intelligence to Human Health and Human Existence,” da Frederik Federspiel, Ruth Mitchell, Asha Asokan, Carlos Umana, da kuma David McCoy suka wallafa.