Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Anna Moneymaker/Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Masanan Kimiyya Sun Tura Ranar Tashin Duniya Zuwa Gaba​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Masanan Kimiyya Sun Tura Ranar Tashin Duniya Zuwa Gaba​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 A ranar 24 ga Janairu, 2023, masana kimiyya sun ce yanzu Agogon Ranar Tashin Duniya a ya yi kusa da tsakar dare, wanda yake nufi karshen duniya.

  •   Kafofin yada labarai na AFP International Text Wire ya sanar cewa: ‘Agogon Ranar Tashin Duniya’ da ke nuna dukan matsalolin ꞌyan Adam ya matsa kusa zuwa tsakar dare a ranar Talata. Abubuwan da ke faruwa a duniya kamar yakin da ake yi a Yukiren da tsoron yakin da za a yi amfani da makaman nukiliya da kuma mumunan yanayi da mahalin duniya yake ciki.”

  •   Kafofin yada labarai na ABC ya sanar cewa: “Masana kimiyya sun fada cewa a ranar Talata an matsar da Agogon Ranar Tashin Duniya zuwa dakikoki 90 kafin tsakar dare, wannan shi ne lokaci da ya fi kusa da ꞌyan Adam suka taba yi zuwa halaka kansu gabaki daya.

  •   Jaridar The Guardian ta ce: “Rukunin masanan kimiyya a fadin duniya sun ce da alama sosai yanzu fiye da dā cewa ꞌyan Adam za su halaka kansu.”

 ꞌYan Adam da duniyar nan za su daina kasancewa nan ba dadewa ba? Muna bukatar mu ji tsoron abin da zai faru a nan gaba? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

Abin da zai faru a nan gaba

 Littafi Mai Tsarki ya ce “duniya tana nan daram har abada” kuma mutane za “su zauna a ciki har abada.” (Mai-Waꞌazi 1:4; Zabura 37:29) Saboda haka, mutane ba za su iya halaka duniya ko kuma su hana mutane rayuwa a ciki ba.

 Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi karshen duniya. Alal misali, ya ce “duniya . . . tana wucewa.”​—1 Yohanna 2:17.

Ka kasance da raꞌayin da ya dace

 Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace duk da matsalolin da ke duniya. Ta yaya zai iya yin hakan?

  •   Littafi Mai Tsarki yana ba mu shawara mai kyau da za ta iya taimaka mana a rayuwarmu ta yau da kullum. (2 Timoti 3:​16, 17) Alal misali, ka karanta tailfin nan “How to Control Worry” don ka ga yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka kasance da raꞌayin da ya dace duk da abubuwan da suke faruwa a duniya.

  •   Littafi Mai Tsarki ya sa mu kasance da bege don nan gaba. (Romawa 15:4) Ya bayyana ainihin abubuwan da za su faru a yau da kuma a nan gaba, hakan zai taimaka mana mu kasance da tabbaci duk da abubuwan da suke faruwa a yau.

 Don ka kara fahimtar abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki, muna so ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da taimakon wani ko wata kyauta a yau.

a Jaridar Bulletin of the Atomic Scientists ta ce: “An tsara Agogon Ranar Tashin Duniya don ya sanar da jamaꞌa cewa mun kusa halaka duniyar da munanan abubuwan da muka kera. Abu ne da ke tuna mana matsalolin da muke da su, kuma wajibi ne mu magance su idan muna so mu rayu a wannan duniya.”