Kaꞌidodin da Za Su Taimake Ka Idan Ka Rasa Aikinka
Idan mutum ya rasa aikinsa, hakan zai sa ba zai samu isashen kudin biyan bukatun iyalinsa, kuma zai rika bakin ciki da damuwa. Bin shawarwari na gaba da aka dauko daga kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da ke da amfani a koyaushe zai taimaka maka ka jimre.
Ka gaya wa mutane yadda kake ji.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “A koyaushe aboki yana nuna kauna.”—Karin Magana 17:17.
Bayan ka rasa aikinka, za ka rika bakin ciki da fushi ko ka rikice, ko kuma ka ji ba ka da amfani. Amma idan ka gaya wa mambobin iyalinka da aminanka, za su iya karfafa ka. Za su iya ba ka shawara mai kyau da za ta taimaka maka ka sami wani aiki.
Ka guji yawan damuwa.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku damu domin gobe, gama gobe yana zuwa da wahalolinsa.”—Matiyu 6:34.
Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu rika yin shiri don nan gaba. (Karin Magana 21:5) Amma ya kuma ba mu shawara cewa mu guji yawan damuwa game da nan gaba. Sau da yawa, muna damuwa a kan abubuwan da watakila ba za su taba faruwa ba. Ya fi kyau mu mai da hankali a kan abin da wajibi ne mu yi kowace rana.
Littafi Mai Tsarki ya ba da wasu shawarwari a kan yadda za ka jimre da matsalar da kake ciki a yanzu. Ka karanta talifin nan “How to Deal With Stress” don ka samu karin bayani.
Ka rage kudin da kake kashewa.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Na san yadda zan zauna . . . cikin rashi ko cikin samu.”—Filibiyawa 4:12.
Ka amince da sabon yanayinka. Hakan ya kunshi rage kudin da kake kashewa. Ka mai da hankali don kada ka ci bashi da ba ka bukata ka ci ba.—Karin Magana 22:7.
Don samun karin bayani a kan yadda za ka yi manajin kudin da kake samu, ka karanta talifin nan “Yadda Za Ka Yi Manejin Kudin da Kake Samu.”
Ka yi amfani da lokacinka da kyau.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi kome da hikima, kuna amfani da kowane zarafin da kuke da shi.”—Kolosiyawa 4:5.
Ko da yake ba ka zuwan aiki kuma, ka yi amfani da lokacinka da kyau. Yin hakan zai sa ka natsu kuma ka ga kana da daraja.
Ka yi shirin yin wani irin aiki.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin dukan aiki akwai lada.”—Karin Magana 14:23.
Ka kasance a shirye ka yi wani aiki dabam da wanda ka yi a dā. Kana iya yin aikin da mutane suke ganin ba shi da amfani ko kuma wanda kudin da za ka samu bai zai kai na dā ba.
Ka nace da neman aiki.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da safe ka shuka hatsinka, da yamma kada ka nada hannuwanka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba.”—Mai-Waꞌazi 11:6.
Ka ci gaba da neman aiki. Ka gaya wa mutane cewa kana neman aiki. Ka gaya wa danginka da abokanka da abokan aikinka na dā da kuma makwabtanka. Ka duba kamfani da ke haya ma wasu kamfanoni masu aiki da masu tallar neman masu aiki da dandalin da ke nuna ko akwai aiki don masu neman aiki. Ka yi shirin zuwa ganawa na neman aiki da yawa da kuma saka aflikeshan da yawa kafin ka samu aiki.