Masana Sun Gano Cewa Sarki Dauda Ya Taba Wanzuwa
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Sarki Dauda na Isra’ila ya yi rayuwa a karni na 11 kafin haihuwar Yesu, kuma zuriyarsa sun yi sarauta na daruruwan shekaru. Amma wasu mutane sun yi shakkar wannan. Sun ce labarin Sarki Dauda kage ne kawai. Amma, Sarki Dauda ya wanzu kuwa da gaske?
A shekara ta 1993, wani masani mai suna Avraham Biran tare da abokan aikinsa sun gano wani gutsuren dutse mai dauke da rubutun nan “Zuriyar Dauda” a Tel Dan, a arewacin Isra’ila. An yi rubutun da tsohon yaren Semitic na karni na 9 kafin zamaninmu. Babu shakka, dutsen gutsuren mutum-mutumi ne da mutanen Aramiya suka gina don su rika tunawa da yakin da suka ci a kan Isra’ilawa.
Wani talifi a Bible History Daily ya ce: Akwai mutanen da suka yi shakkar rubutun nan ‘Zuriyar Dauda’ . . . Amma yawancin masanan Littafi Mai Tsarki da kuma masu tona kasa sun amince cewa rubutun da ke gutsuren dutsen ya tanadar da cewa Sarki Dauda wanda labarinsa ke cikin Baibul ya wanzu da gaske. Wannan yana cikin labari mafi muhimmanci da masana suka rahoto a BAR [Biblical Archaeology Review].”