Ta’addanci Zai Taba Karewa Kuwa?
Bayan ’yan ta’adda sun kai hari, mukan tambayi kanmu cewa: ‘Allah ya damu da mutane kuwa? Me ya sa wadannan abubuwan suke faruwa? Ta’addanci a zai taba karewa kuwa? Ta yaya zan shawo kan tsoron da nake ji?’ Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa.
Yaya Allah yake ji game da ta’addanci?
Allah ya tsani tashin hankali da kuma ta’addanci. (Zabura 11:5; Karin Magana 6:16, 17) Kuma Yesu wanda yake wakiltar Allah ya ja kunnen mabiyansa a lokacin da suka so su kai ma wasu mutane hari. (Matiyu 26:50-52) Ko da yake wasu suna da’awar cewa suna kai ma wasu hari ne a sunan Allah, amma Allah bai umurce su su yi hakan ba. Ban da haka, ba ya ma amsa addu’o’insu.—Ishaya 1:15.
Allah ya damu da duk wadanda suke shan wahala har da wadanda ’yan ta’adda suka kai wa hari. (Zabura 31:7; 1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Allah zai dauki matakin kawo karshen tashin hankali da kuma zalunci.—Ishaya 60:18.
Abin da ke jawo ta’addanci
Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ke jawo ta’addanci ya ce: “Na ga wani yana da iko a kan wadansu, ikon kuwa ya cuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Mutane sun dade suna amfani da ta’addanci don su ci zalin wasu. A sakamakon irin wannan zaluncin, wasu suna yin amfani da ta’addanci don samun mafita.—Mai-Wa’azi 7:7.
Za a kawo karshen ta’addanci
Allah ya yi alkawari cewa, zai kawar da tsoro da ta’addanci, kuma zai kawo salama a nan duniya. (Ishaya 32:18; Mika 4:3, 4) Allah ya ce:
Zai kawar da abin da ke kawo ta’addanci. Allah zai sauya gwamnatin ’yan Adam da gwamnatinsa. Wanda zai yi mulki a wannan gwamnati, wato Yesu Kristi zai yi wa kowa adalci kuma zai kawar da ta’addanci da zalunci. (Zabura 72:2, 14) A wannan lokacin, babu wanda zai yi ta’addanci. Mutane za “su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”—Zabura 37:10, 11.
Zai kawar da dukan abin da ta’addanci ya jawo. Allah zai warkar da mutanen da ta’addanci ya shafa, ko ya yi musu illa. (Ishaya 65:17; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4) Ya yi alkawari cewa zai tā da wadanda suka mutu zuwa rayuwa a duniya cike da salama.—Yohanna 5:28, 29.
Littafi Mai Tsarki ya ba mu dalilai musu kyau da suka nuna cewa nan ba da dadewa ba Allah zai dauki mataki. Amma kana iya tunanin cewa, ‘Me ya sa Allah bai riga ya kawar da ta’addanci ba?’ Don ka sami amsar, ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Kyale Mutane Su Sha Wahala?
a “Ta’addanci” yana nufin tsoratar da mutane don kawo canji a gwamnati ko a addini ko kuma a yadda mutane suke bi da juna. Amma wasu mutane za su iya cewa wasu matakan da ake dauka ba ta’addanci ba ne.