Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

sinceLF/E+ via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Wa Zai Ceci ꞌYan Farar Hula?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Wa Zai Ceci ꞌYan Farar Hula?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoto cewa:

  •   Daga ranar 7 ga Oktoba zuwa 23 ga Oktoba 2023, yakin Israꞌila da Gaza ya jawo mutuwar mutane fiye da 6,400 kuma mutane 15,200 ne suka ji rauni, yawancinsu ꞌyan farar hula ne. Kari ga haka, an tilasta wa mutane dubbai su bar gidajensu.

  •   A ranar 24 ga Satumba, an gano cewa yaki tsakanin Rasha da Yukiren ya jawo mutuwar ꞌyan farar hula 9,701 kuma mutane 17,748 ne suka ji rauni a Yukiren.

 Wane alkawari ne Littafi Mai Tsarki ya yi ma wadanda suke shan wahala saboda yaki?

Dalilin kasancewa da bege

 Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai kawo karshen “yake-yake a dukan duniya.” (Zabura 46:9) Zai yi amfani da mulkinsa don ya kawar da dukan gwamnatocin ꞌyan Adam. (Daniyel 2:44) Mulkin Allah zai sa ꞌyan Adam su daina shan wahala.

 Ga abin da Yesu Kristi, Sarkin Mulkin Allah zai yi:

  •   Zai “kubutar da masu bukata yayin da suka yi kira, da matalauta da kuma marasa taimako. Yakan ji tausayin marasa karfi da masu bukata, yakan ceci rayukan matalauta. Daga masu danniya da masu tā da hankali yakan fanshe su.”​—Zabura 72:​12-14.

 Ta wurin Mulkinsa, Allah zai kawar da zalunci da wahalar da yake-yake da mugunta suke jawowa.

  •   “Zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun bace.”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

 Nan ba da dadewa ba, Mulkin Allah zai yi canje-canje sosai a duniya. Tun da dadewa, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi “yake-yake da jita-jitarsu” da suke faruwa a yau. (Matiyu 24:6) Wannan da wasu abubuwan da suke faruwa sun nuna cewa muna “kwanakin karshe” na sarautar ꞌyan Adam.​—2 Timoti 3:1.