Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Chris McGrath/Getty Images

WAꞌAZI NA MUSAMMAN

Yake-Yake​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Yake-Yake​—Abin da Mulkin Allah Zai Yi

 A fadin duniya, yake-yake sun ci gaba da sa mutane shan wahala. Ga wasu rahoto:

  •   A ranar 7 ga Yuni, 2023, wata kungiyar bincike da ake kiran Peace Research Institute Oslo ta ce: “A shekarar da ta shige, karin mutane sun mutu domin yake-yake, musamman a Ethiopia da Yukiren.”

  •   A ranar 8 ga Fabrairu, 2023, The Armed Conflict Location & Event Data Project (ACLED) sun ce: “Yakin da ake yi a Yukiren daya ne daga cikin yake-yake da suka yi muni a shekara ta 2022. A duk fadin duniya tashin hankali don siyasa ya karu da kashi 27 bisa 100 a shekarar da ta shige, kuma ya shafi mutane wajen biliyan 1.7.”

 Littafi Mai Tsarki yana sa mu kasance da bege. Ya ce: “Allah na sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taba rushewa ba.” (Daniyel 2:44) A Mulkin ko gwamnatin ne Allah zai “tsai da yake-yake a dukan duniya.”​—Zabura 46:9.