Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

hadynyah/E+ via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Yaki da Canjin Yanayi Sun Jawo Karancin Abinci a Duniya​—Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

Yaki da Canjin Yanayi Sun Jawo Karancin Abinci a Duniya​—Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

 Yakin da ake yi a Yukiren tare da sakamakon canjin yanayi, sun ci-gaba da jawo rashin isashen abinci a duniya. Abin da ke faruwa ke nan musamman a kasashen da suke tasowa a fannin tattalin arziki, kuma yana yi mutane da yawa wuya a kasashen nan su sami isashen abinci.

  •   A ranar 17 ga Yuli, 2023, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce: “Yaki da kuma canjin yanayi da sauransu suna sa ba a samun isashen abinci kuma.”

  •   A ranar 23 ga Yuli, 2023, jaridar Atalayar.com kuma ta ce: “Rasha ta cire kanta daga yarjejeniya da aka yi na fitar da hatsi daga kasarta zuwa wurare dabam-dabam. Masana suna ganin cewa hakan zai sa rashin abincin ya yi muni har ya sa abinci ya zama da tsada a kasashe da aka fi talauci, musamman a Arewacin Afrika da kuma Gabas ta Tsakiya.”

 Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da rashin abinci da kuma rayuwa a nan gaba.

Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da yunwa

  •   Yesu ya annabta cewa “Alꞌumma za ta tasar wa alꞌumma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa.”​—Matiyu 24:7.

  •   Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna ya bayyana wasu mahayan doki guda hudu. Daya daga cikinsu yana wakiltar yaki. Nabiye da shi kuma yana wakiltar yunwa wato lokacin da za a yi rashin abinci kuma a sayar da su da tsada. “Da na duba, sai ga wani bakin doki. Mai hawansa yana rike da maꞌauni a hannunsa. Sai na ji wani abu mai kama da murya . . . tana cewa, ‘Mudun hatsin alkama na yawan kudin da lebura zai samu na aiki yini daya, mudu uku na hatsin bale na yawan kudin da lebura zai sami na aiki yini daya.’ ”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​5, 6.

 A kwanakin nan da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanakin karshe,” annabce-annabce game da yunwa suna cikawa. (2 Timoti 3:1) Don samun karin bayani game da “kwanakin karshe” da mahayan doki guda hudu na Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, ka kalli bidiyon nan Duniya Ta Canja Sosai Tun Daga 1914 kuma ka karanta talifin nan “Su Wane ne Mahaya Hudun?

Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka

  •   Littafi Mai Tsarki na dauke da shawarwari masu kyau da za su iya taimaka mana mu jimre da yanayoyi masu wuya, kamar tsadan abinci da kuma rashin isashen abinci. Ga wasu misalai a talifin nan “Yadda Za Ka Yi Manejin Kudin da Kake Samu.”

  •   Littafi Mai Tsarki ya kuma ba mu begen cewa abubuwa za su gyaru. Ya yi mana alkawari cewa za “a sami hatsi a yalwace a kasar” kuma hakan yana nufin kowa zai ci ya koshi. (Zabura 72:16) Don samun karin bayani game da alkawarin nan da kuma yadda za ka gaskata da shi, ka karanta talifin nan “A Real Hope for a Better Tomorrow.”