Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Yakin Yukiren Ya Dada Jawo Karancin Abinci a Duniya

Yakin Yukiren Ya Dada Jawo Karancin Abinci a Duniya

 A ranar 19 ga Mayu, 2022, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun ji daga bakin fiye da maꞌaikatan gwamnati 75 cewa, “sanaddiyar annobar korona da canjin yanayi an sami karancin abinci, amma yanzu, yakin Yukiren yana dada sa matsalar ta yi muni a fadin duniya.” Ba da dadewa ba bayan haka, mujallar The Economist ta ce, “da yake duniya tana cike da matsaloli da ma, wannan yakin zai sa a dada samun matsalar yunwa.” Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa za a sami karancin abinci a zamaninmu, amma ya ba mu shawarwarin da za su taimaka mana mu jimre.

Annabcin Littafi Mai Tsarki game da karancin abinci

  •    Yesu ya ce: ‘Alꞌumma za ta tasar wa alꞌumma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa.’​—Matiyu 24:7.

  •    Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna ya ba da misali da wasu mahaya hudu. Daya daga cikin mahayan yana wakiltar yaki. Bayan shi kuma sai wanda yake wakiltar yunwa, wato lokacin da za a yi karancin abinci kuma su yi tsada sosai. “Da na duba, sai ga wani bakin doki. Mai hawansa yana rike da maꞌauni a hannunsa. Sai na ji wani abu mai kama da murya . . . tana cewa, ‘Mudun hatsin alkama na yawan kudin da lebura zai samu na aiki yini daya, mudu uku na hatsin bale na yawan kudin da lebura zai sami na aiki yini daya.’ ”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​5, 6

 Wadannan annabcin game da karancin abinci suna cika yanzu a zamaninmu da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanakin karshe.” (2 Timoti 3:1) Don karin bayani game da “kwanakin karshe” da kuma mayahan da aka ambata a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, ka kalli bidiyon nan, Duniya Ta Canja Sosai Tun Daga 1914 kuma ka karanta talifin nan, “Mahaya Hudu​—Su Wane ne Mahaya Hudun?

Yadda Littafi Mai Tsarki yake taimakawa

  •    A Littafi Mai Tsarki, akwai shawarwari masu kyau da za su iya taimaka mana mu jimre da matsaloli, har da karancin abinci da kuma tsadan abinci. Ga misalin su a talifin nan, “Yadda Za Ka Yi Manejin Kudin da Kake Samu.”

  •    Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa abubuwa za su gyaru. An yi alkawari cewa a nan gaba za “a sami hatsi a yalwace a kasar” kuma kowa zai sami abinci da zai ci ya koshi. (Zabura 72:16) Don ka ga wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce game da nan gaba da kuma dalilin da ya sa za ka gaskata da hakan, ka karanta talifin nan, “A Real Hope for a Better Tomorrow.”