Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Karancin Abinci a Duniya?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Karancin Abinci a Duniya?

 “Isashen abinci.” Wannan shi ne abin da shugabannin duniya suke da burin cim mawa don su magance wata babbar matsala da ꞌyan Adam suke fuskanta, wato suna so su sa a sami isashen abinci a duk fadin duniya. a Amma, za a daina yunwa a duniya? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

Littafi Mai Tsarki ya annabta yunwa da ake yi a yau

 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi yunwa a zamaninmu da ya kira “kwanakin karshe.” (2 Timoti 3:1) Ba Allah ne ya sa ake yunwa a duniya ba, amma ya gaya mana game da hakan. (Yakub 1:13) Ga wasu annabce-annabce guda biyu.

 Za a kuma yi yunwa . . . a wurare dabam-dabam.” (Matiyu 24:7) Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi yunwa a wurare da yawa. Mutanen da suke bincike game da yadda ake sarrafa da kuma rarraba abinci, sun ba da rahoto cewa: “Yunwa da rashin isashen abinci da kuma samun abinci masu gina jiki suna kara muni.” b Miliyoyin mutane a kasashe dabam-dabam ba sa samun abincin da suke bukata. Kuma hakan ya sa da yawa a cikinsu suna mutuwa.

 Da na duba, sai ga wani bakin doki. Mai hawansa yana rike da maꞌauni a hannunsa.” (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:5) A annabcin nan doki da mai hawansa suna wakilta yunwa a kwanakin karshe. c Mai hawan dokin yana rike da maꞌauni a hannunsa kuma yana amfani da shi don ya auna abinci don kowa ya dan samu. Bayan hakan sai wata murya ta fito tana cewa farashin abinci zai karu kuma ya gargadi mutane su dinga adana abinci. (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:6) Kuma abin da yake faruwa a yau ke nan, domin biliyoyin mutane ba sa iya samun ko kuma su saya abinci masu gina jiki.

Yadda ba za a sake yunwa ba

 Masana sun ce: Abincin da ake samu a duniya zai iya ciyar da dukan mutane a duniya. To, mene ne yake jawo karancin abinci? Kuma mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce Mahaliccinmu Jehobah d zai yi don ya magance wadannan matsalolin?

 Matsala:Shugabanni ba za su iya kawo karshen talauci, ko rashin adalcin da ke sa mutane yunwa ba.

 Mafita: Za a halaka gwamnatocin ꞌyan Adam, kuma Mulkin Allah zai kasance har abada. (Daniyel 2:44; Matiyu 6:10) A yau, mutane da yawa ba sa cika samun abinci. Amma, a Mulkin Allah abubuwa za su canja. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu Kristi wanda shi ne Sarkin Mulkin Allah: “Gama yakan kubutar da masu bukata yayin da suka yi kira, da matalauta da kuma marasa taimako. . . . ‘Za a sami hatsi a yalwace a kasar, a sa amfanin gona ya rufe kan tuddai.’ ”​—Zabura 72:​12, 16.

 Matsala: Yake-yake na lallace tattalin arziki, kuma hakan na sa ya yi wa mutane wuya su sami abincin da suke bukata.

 Mafita: Jehobah zai “tsai da yake-yake a dukan duniya, ya kakkarye baka, ya lalatar da māshi, ya kone garkuwa da wuta. (Zabura 46:9) Allah zai halaka makaman yaki tare da wadanda suke sa a yi yaki. Hakan zai sa ya yi sauki kowa ya sami abinci. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa: “A cikin kwanakinsa mai-adalci za shi yalwata; Da salama mai-yawa.”​—Zabura 72:​7, Tsohuwar Hausa a Saukake.

 Matsala: Yanayoyi masu tsanani da balaꞌoꞌi suna lalata amfanin gona da kuma kakashe dabbobi.

 Mafita: Allah zai magance balaꞌoꞌi kuma ya sa duniya ta zama wurin da za a sami amfanin gona da kyau sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Jehobah] ya kwantar da iska mai karfi, rakuman ruwa kuma suka kwanta shiru. . . . Ya mai da hamada tafkin ruwa, busasshiyar kasa kuma mabubbugar ruwa. Can ya zaunar da masu jin yunwa . . . Suka nome gonaki suka shuka inabi, suka girbe amfanin gona a yalwace.

 Matsala: Mugaye sukan sayar da abincin da ba shi da kyau, ko kuma su hanna mutane samun abincin da suke bukata.

 Mafita: Mulkin Allah zai halaka mugayen mutane. (Zabura 37:​10, 11; Ishaya 61:8) Littafi Mai Tsarki ya bayyana Jehobah Allah cewa shi ne “wanda yakan yanke sharꞌia ga wadanda ake musu danniya, wanda yakan ba da abinci ga masu jin yunwa.”​—Zabura 146:7.

 Matsala: A kowace shekara, ana barnar kashi talatin da uku cikin dari na abinci.

 Mafita: A Mulkin Allah, za a sami abinci a yalwace. Yayin da Yesu yake duniya, ya yi kokari ya sa kada a bata abinci. Alal misali, akwai ranar da Yesu ya ba mutane fiye da 5,000 abinci. Jim kadan bayan hakan, sai ya gaya wa almajiransa cewa: ‘Ku tattara gutsattsarin da suka ragu domin kada kome ya lalace.’​—Yohanna 6:​5-13.

 Mulkin Allah zai kawar da abubuwan da suke jawo yunwa, hakan zai sa dukan ꞌyan Adam su more abinci masu gina jiki da yawa. (Ishaya 25:6) Don ka koya game da lokacin da Mulkin Allah zai cim ma hakan, ka duba talifin nan “Yaushe Ne Mulkin Allah Zai Zo Duniya?

a A shekara ta 2015, kasashen da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya sun kafa tsarin abubuwa da za su so su cim ma daga shekara ta 2015 zuwa 2030.

b Rahoton da aka samu daga Kungiyar Abinci da Noma na Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar International Fund for Agricultural Development, da United Nations Children’s Fund, da United Nations World Food Programme, da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya.

c Don samun karin bayani game da mahaya hudu da aka ambata a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, ka karanta talifin nan “Su Wane ne Mahaya Hudun?

d Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Ka karanta talifin nan “Wane ne Jehovah?