Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

MILTIADIS STAVROU | TARIHI

“Mun Mori Ja-gorancin Jehobah da Kuma Kulawarsa”

“Mun Mori Ja-gorancin Jehobah da Kuma Kulawarsa”

A lokacin da nake shekara 13, kamar sauran matasa, ina jin dadin kallon motocin da suke wucewa a titin da ke unguwarmu a Tripoli, a kasar Lebanon. A cikin motocin akwai wadda ta burge ni sosai, wata kyakkyawar jar mota kirar Amirka na wani mutumin Syria. Na yi mamaki sosai saꞌad da firist na cocinmu na Orthodox ya umarce mu cewa mu jejjefi motar da duwatsu domin mai motar Mashaidin Jehobah ne!

 Sai muka ce wa firist din, hakan zai iya ja ma direban rauni. Amma ya ce: “Ku kashe shi, sai ku share jininsa da ke hannayenku a riga na!” Ko da yake, ina son cocinmu na Greek orthodox sosai, abin da ya fada ya sa na daina zuwa cocin. Abin da ya faru a ranar ya taimaka min in gane gaskiya game da Jehobah.

Sanin Gaskiya Game da Jehobah

 A lokacin da nake girma, birnin Tripoli na cike da mutane daga al’adu da kabilu da kuma addinai dabam-dabam. Kowane iyali na alfahari da inda suka fito ko garinsu, iyalinmu ma ba a bar su a baya ba. Ni da yayuna mun hada kai da wata kungiya da ake kira, Soldiers of the Faith a (Sojojin Imani) da suke gāba da Shaidun Jehobah. Ko da yake ba mu taba haduwa da Shaidun ba, amma firist namu ya ce su wata kungiya ce da take gāba da cocinmu na Greek Orthodox kuma shugabansu wani ne da ake kira Jehobah. Kullum firist namu yana ce mana mu kai ma Shaidun hari a duk lokacin da muka hadu da su.

 Ko da yake ban sani ba, ashe ꞌyanꞌuwana uku sun riga sun taba haduwa da Shaidun Jehobah. Amma maimakon yin fada da su, ꞌyanꞌuwana sun yarda su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su domin su karyata su. Wata rana da na dawo gida da yamma, sai na ga dakinmu cike da Shaidu suna tattaunawa daga cikin Littafi Mai Tsarki da mutanen gidanmu da kuma wasu makwabtanmu. Abin ya bata min rai! Kuma na ce ‘me ya sa ꞌyanꞌuwana za su ci amanar cocin Orthodox haka? Da zan fita sai wani makwabcinmu wanda sanannen likitan hakori ne kuma shi Mashaidi ne ya ce min in zauna, kuma in kasa kunne. Na ji daya daga cikinsu yana karanta Zabura 83:18 daga Littafi Mai Tsarkina, daga nan ne na gano cewa firist na mu ya yi mana karya. Ashe Jehobah ba shugaban wani kungiya ba ne, Allah Makadaici ne na gaskiya.

Jim kadan bayan na yi baftisma

 Na so in kara sanin abubuwa game da Jehobah, sai na soma zuwa nazarin Littafi Mai Tsarki da ake yi a gidanmu, wanda Danꞌuwa Michel Aboud yake gudanarwa. Wata rana, wani abokina ya yi wata tambaya kuma tambayar ta dade tana damuna tun ina yaro. Ya ce: “Ka gaya mana, wane ne ya halicci Allah?” Danꞌuwa Aboud ya nuna mana wani kule da ke kwance a kan kujera. Sai ya ce kuliyoyi ba sa fahimtar abin da ꞌyan Adam suke fada ko yadda suke tunani ba. Hakazalika, ba za mu iya fahimtar abubuwa da yawa game da Allah ba. Wannan kwatancin ya sa na fahimci cewa akwai wasu abubuwa game da Jehobah da ba za mu iya fahimta ba. Ba da dadewa ba, na yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma na yi baftisma a 1946 saꞌad da nake dan shekara 15.

Yin Majagaba Ya Taimaka Min a Rayuwa

 A 1948, na soma aikin daukan hoto tare da danꞌuwana Hanna. Shagonsa na kusa da shagon wani danꞌuwa mai suna Najib Salem b da yake sanaꞌar zane. Najib mai waꞌazi da kwazo ne sosai kuma ba ya jin tsoro. Ya ci gaba da zama da irin halin nan har lokacin da ya mutu a shekara 100. Idan na bi shi waꞌazi a wasu kauyuka, ina ganin yadda yake waꞌazi da kwazo duk da cewa ana tsananta mana. Kuma yana iya soma magana da kowa game da Littafi Mai Tsarki ko da su ꞌyan wane addini ne. Halinsa ya taimaka min sosai.

Najib Salem (a baya ta dama) shi ne ya taimaka min sosai

 Wata rana, da nake wurin aiki, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Mary Shaayah ta ziyarce mu. Ita ꞌyar Lebanon ce amma ta zama a kasar Amirka. Duk da cewa ita uwa ce kuma tana da ayyuka da yawa, tana hidimar majagaba. Ziyarar da ta kawo mana ne ya sa na canja salon rayuwata. Mary ta yi fiye da awa biyu tana gaya mana abubuwan da take morewa a hidimarta. Kafin ta tafi, Mary ta kalle ni kuma ta ce: “Milto, tun da ba ka da aure, me zai hana ka yin hidimar majagaba?” Sai na ce ba zan iya ba don sai na nemi kudin biyan bukatu na yau da kullum. Sai ta tambaye ni cewa: “Awa nawa na yi tare da ku da safen nan?” Sai na ce: “Wajen awa biyu.” Mary ta ce: “Ban gan ka kana wani aiki sosai tun lokacin da na zo ba. Don haka, idan kana amfani da lokaci kamar hakan kowace rana kana waꞌazi, za ka iya hidimar majagaba. Ka gwada yi na shekara daya mana ka ga ko za ka iya yi ko aꞌa.”

 Ko da yake yana da wuya maza su karbi shawara daga wurin mace a alꞌadarmu, amma na ga kamar shawarar da ta ba ni yana da kyau. Bayan wata biyu a Janairu 1952 na soma hidimar majagaba. Bayan watanni 18, an gayyace ni zuwa aji na 22 a Makarantar Gilead.

ꞌYanꞌuwa da abokan arziki suna min ban-kwana da zan tafi makarantar Gilead a 1953

 Bayan na sauke karatu, an tura ni zuwa Gabas ta Tsakiya. Bai kai shakara daya ba, sai na auri Doris Wood, wata ꞌyarꞌuwa mai faraꞌa daga Ingila, ita ma tana hidimar masu waꞌazi a kasashen waje a Gabas ta Tsakiya.

Yin Wa’azi a Syria

 Ba da dadewa ba, bayan aurenmu sai aka tura mu hidima a Aleppo, da ke Syria. Da yake an sa takunkumi a hidimarmu, wadansu ne suke hada mu da yawancin wadanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki tare da su.

 Wata rana, mun ziyarci wata da ta nuna cewa tana so ta koyi abin da ke Littafi Mai Tsarki. Ta bude mana kofa da rawan jiki sai ta ce: “Ku rika kula sosai! Yanzu ꞌyan sanda suka bar nan. Suna so su san inda kuke zama.” Ba shakka, ꞌyan sandan sun san wuraren da muke zuwa yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Da muka gaya ma ꞌyanꞌuwan da suke kula da aikinmu a Gabas ta Tsakiya, sai suka ce mu bar kasar da wuri. Ko da yake ba mu ji dadin yadda za mu bar daliban da muke koya musu Littafi Mai Tsarki ba, mun ga yadda Jehobah yake kāre bayinsa.

Jehobah Ne Ya Ja-gorance Mu a Iraki

 An tura mu Baghdad a Iraki a 1955. Ko da yake da hikima muke yi wa mutane waꞌazi a Iraki, mun fi mayar da hankali ga Kiristocin.

Tare da masu waꞌazi a kasashen waje, da muke Iraki

 Muna kuma kokarin tattaunawa da Musulman da muka hadu a kasuwa ko a hanya. Doris takan fara da wani batun da zai iya jan hankalin mutanen da ta hadu da su. Alal misali, takan ce: “Babana yakan ce dukanmu za mu tsaya a gaban Mahaliccinmu.” (Romawa14:12) Sai ta kara da cewa: “Yin tunani a kan abin da ya fada yakan taimaka min. Mene ne raꞌayin ka?”

 Mun ji dadin hidimarmu a Baghdad kusan shekara uku, muna taimaka wa ꞌyanꞌuwa a kan yadda za su rika yin waꞌazi da basira. A gidanmu na masu waꞌazi a kasashen wajen ne muke taro da Larabci. Mun yi farin ciki sosai a lokacin da wasu mutane suka zo taronmu daga unguwar Assuriyawa, kuma yawacin mutanen da suke zama a wurin suna zuwa coci. Da suka ga irin kauna da kuma hadin kai da muke da shi a taronmu, sai suka gane cewa mu ne mabiyan Yesu na gaskiya.​—Yohanna 13:35.

A gidan masu waꞌazi a kasashen waje ne muke taro a Baghdad

 Daya daga cikin wadanda suka yi saurin fahimtar waꞌazinmu shi ne, Nicolas Aziz, shi mutum ne mai hankali da saukin kai, yana da iyali kuma shi dan asalin Armaniya ne da Assuriya. Ba tare da bata lokaci ba, Nicolas da matarsa Helen sun amince da gaskiyar da suka koya daga Littafi Mai Tsarki game da Jehobah da Dansa Yesu. (1 Korintiyawa 8:​5, 6) Na tuna ranar da Nicolas da kuma wasu mutane 20 suka yi baftisma a Kogin Yufiretis.

Mun Ga Yadda Jehobah Ya Taimaka Mana a Iran

A 1958, lokacin da muke Iran

 Bayan juyin mulki kuma aka kashe Sarki Faisal na 2, a ranar 14 ga Yuli, 1958 a Iraki, mun kaura zuwa Iran. A can muka ci gaba da hidimarmu tsakanin bakin da muka samu a wurin na wajen wata shida.

 Kafin mu bar Tehran, babban birnin kasar, an kai ni offishin ꞌyan sanda don a yi min wasu tambayoyi. Hakan ya sa na san cewa ꞌyan sanda suna bibiyanmu. Bayan an gama min tambayoyi, sai na kira Doris kuma na gaya mata cewa ta yi hattara don ꞌyan sanda suna bibiyanmu. Ganin irin hatsarin da rayukanmu suke ciki, sai muka yanke shawara cewa ba zan dawo gida ba, kuma ba za mu kasance tare ba na dan lokaci, sai lokacin da za mu bar kasar.

 Doris ta nemi wani wuri ta zauna har zuwa lokacin da muka hadu a tashar jirgin sama. Amma yaya za ta iso tashar jirgin ba tare da an gan ta ba? Doris ta yi addu’a ga Jehobah game da batun.

 Sai kawai aka soma tafka ruwan sama da ya sa kowa neman wurin buya, har ma da ꞌyan sandan. Hakan ya sa koꞌina ya yi shiru, sai Doris ta sami dama ta soma tafiya. Doris ta ce, “Wannan ruwan saman daga Allah ne!”

 Bayan mun bar lran, sai aka tura mu zuwa wani yanki, inda muke iya yi wa mutane daga kabilu da kuma addinai dabam-dabam waꞌazi. A shekara ta 1961, mun soma aikin kula da daꞌira, kuma hakan ya ba mu dama mu ziyarce ꞌyanꞌuwa a wurare dabam-dabam da ke Gabas ta Tsakiya.

Ruhun Mai Tsarki Daga Wurin Jehobah Ya Taimaka Mana

 Na samu dama da yawa da suka nuna min yadda ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu kasance da hadin kai a hidimarmu a Gabas ta Tsakiya. Na tuna yadda muka ji dadin tattaunawa daga Littafi Mai Tsarki da Eddy da Nicolas wasu ꞌyan Falasdinu. Su biyun suna ji dadin zuwa taronmu, amma ba da dadewa ba sun daina nazarin Littafin Mai Tsarki, domin suna da tsattsauran raꞌayin game da siyasa. Na yi adduꞌa Allah ya taimaka musu su gane gaskiya. Da suka gane cewa Allah ne zai iya magance matsalolinmu, ba na mutanen Falasdinu kadai ba amma na dukan ꞌyan Adam, sai suka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 2:4) Sun daina tunani cewa mutanensu ne suka fi sauran daraja kuma suka baftisma. Daga baya, Nicolas ya zama mai kula da daꞌira.

 Yayin da muke ziyartar ꞌyanꞌuwa daga kasa zuwa kasa, ganin yadda ꞌyanꞌuwa suke kasancewa da aminci duk da yanayinsu yana burge ni da matata Doris sosai. Da yake na san suna kokarin jimre matsaloli da dama, ina kokari in karfafa su a duk lokacin da muka ziyarce su a matsayin mai kula da daꞌira. (Romawa 1:​11, 12) Domin in cim ma hakan, nakan tuna wa kaina cewa ban fi ꞌyanꞌuwan da muke ziyarta daraja ba. (1 Korintiyawa 9:22) Ina jin dadin karfafa ꞌyanꞌuwan da suke bukatan karfafa.

 Abin farin cikin ne sanin cewa yawancin wadanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su, sun zama bayin Jehobah masu aminci. Wasu daga cikin su sun yi gudun hijira tare da iyalansu zuwa wasu kasashe don ana yaki a kasarsu. Amma hakan ya taimaka sosai a bangarorin da ake yin Larabci a wurare kamar su, Australiya da Kanada da Turai da kuma Amirka. A ꞌyan shekarun baya bayan nan, wasu daga cikin yaransu da suka yi girma, sun sake komawa Gabas ta Tsakiya domin su yi hidima a inda ake bukatar masu shela masu karfin hali. Abin farin ciki ne yadda ni da matata Doris muke kewaye da yara da kuma jikoki da suke nan kamar namu!

Mun Dogara ga Jehovah Har Abada

 A duk rayuwanmu, mun ga yadda Jehobah ya kula da kuma yi mana ja-gora a hanyoyi da dama. Na gode da yadda ya taimaka min na daina nuna wariya da kuma kishin kasarmu, wato raꞌayin da nake da shi saꞌad da nake girma. Yadda ꞌyanꞌuwa masu karfin hali da kuma kaunar mutane suka koyar da ni ya taimaka min in koyar da mutanen da suka fito daga wurare dabam-dabam. Yayin da muke kaura daga wata kasa zuwa wata kasa, ni da matata Doris mun fuskanci matsaloli da yawa. Amma hakan ya koya mana yadda za mu dogara ga Jehobah ba ga kanmu ba.​—Zabura 16:8.

 Idan na tuna shekaru da yawa da na yi ina hidimar Jehobah, sai in ga cewa Jehobah ya taimaka min sosai kuma ina bukata in ci gaba da nuna godiya. Na yarda da abin da masoyiyata Doris takan fada cewa, bai kamata mu bar wani abu ya hana mu ibadarmu ga Jehobah ba, ko da ana barazanar kashe mu! Za mu ci gaba da nuna godiyarmu ga Jehobah da ya ba mu dama mu yi waꞌazi a Gabas ta Tsakiya. (Zabura 46:​8, 9) Da gaba gadi, muna jiran yadda abubuwa za su kasance a nan gaba, don mun san cewa Jehobah zai ci gaba da kāre da kuma yi wa bayinsa ja-goranci.​—Ishaya 26:3.

a Domin samun karin bayani game da kungiyar nan, ka dubi, 1980 Yearbook of Jehovah’s Witnesses shafi na 186-188.

b Za ka iya samun tarihin Najib Salem a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Satumba, 2001, shafi na 22-26 na Turanci.