Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Aikin Agaji da Aka Yi don Cutar Korona a Dukan Duniya

Aikin Agaji da Aka Yi don Cutar Korona a Dukan Duniya

1 GA YULI, 2021

 A Maris 2020, a lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi sanarwa cewa cutar korona ta zama annoba, mutane da yawa ba su yi tsammani cewa fiye da shekara daya bayan haka annobar za ta ci gaba da damun mutane ba. Annobar ta kama miliyoyin mutane, ta jawo karancin kudi kuma ya shafi yadda mutane suke ji. Ta yaya Shaidun Jehobah suka tsara agaji a lokacin annobar?

Ba da Agaji ga Wadanda Suke da Bukata

 A karkashin ja-gorancin Kwamitin Masu Tsara Ayyuka na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, an kafa Kwamitin Ba da Agaji (DRC) fiye da 950 a fadin duniya saboda annobar korona. A wasu lokuta, sukan gaya wa ’yan’uwa a yankin su taimaka wa juna, a wasu lokuta kuma sukan nuna musu yadda za su sami tallafin gwamnati. Kari ga haka, kwamitocin sun tsara yadda za a ba da agaji ga mutane da yawa da bala’i ya shafa.

 Ga wani labari daga kasar Paraguay da ya nuna hakan. Wata jarida ta ba da rahoto cewa saboda koma bayan tattalin arziki da annobar ta jawo, “ ’yan kasar Paraguay da yawa suna kwana da yunwa.” Amma tuni Kwamitin Ba da Agaji da ke kasar Paraguay ya riga ya soma rarraba akwatunan tallafi na tsawon mako biyu ga iyalai guda hudu. Akwatunan suna dauke da isasshen abinci da kayan shara da kuma kayayyakin tsabtacce jiki. Ana sayan kowane akwati a kan dala 30.

 Ta yaya masu aikin agajin suke kāre kansu da ma wasu daga annobar yayin da suke aikin? Suna saka takunkumin fuska kuma suna ba da tazara sosai tsakaninsu da mutane. Kari ga haka, suna tabbata cewa kamfanin da ke sayar da abincin suna yin abincin a wuri mai tsabta kuma suna bin ka’idodin kiyaye lafiya. Hakan ya kunshi tabbata cewa masu yin abincin suna saka kayan kariya, suna tsabtace da kuma amfani da sabulun kashe kwayoyin cuta a cikin motar daukan kayan kuma a kan wuraren da ake adana abincin. A karshe wadanda suke rarraba abincin suna ba da tazara tsakaninsu da mutane.

Ba A Bata Kudi

 Zuwa Janairu 2021, Kwamitin Masu Tsara Ayyuka ya ba izini a kashe dala million 25 a kan agaji don annobar korona. Rassan ofisoshinmu da Kwamitin Ba da Agaji suna hankali da kudaden da aka bayar saboda gudummawa kuma suna iya kokarinsu su yi tayin farashin kayayyakin da suke so su saya. Alal misali, a kasar Chile, wasu ’yan’uwa da suke tsara aikin agaji sun so su kilo 750 na wani irin wake. Amma a cikin wata daya kawai kudin waken ya ninka farashinsa sau biyu! Awoyi biyu su sayi waken a sabon farashin, sai mai sayarwa ya sanar da su cewa wani da ya sayi waken kafin lokacin ya mayar da waken. Saboda haka, maimakon ya caje su farashin da ya haura din, ya yarda cewa zai sayar musu a farashi na dā da mutumin ya saya!

 Amma da ’yan’uwanmu suka je su karbi waken sai mai sayarwan ya ki, don a cewarsa, ’yan’uwanmu suna rashin adalci a yadda suke rarraba waken, kamar yadda wasu kungiyoyi ma suke yi. Daya daga cikin ’yan’uwan ya yi gajeriyar addu’a sa’an nan ya gaya wa mutumin cewa an riga an tantance ko su waye ne suke bukatar taimako a kowace ikilisiya. Kari ga haka, ’yan’uwan sun bayyana wa mutumin cewa da yake ’yan’uwan da za a rarraba musu kayayyakin suna wurare dabam-dabam ne, an shirya kayayyakin bisa ga yanayin wurin da suke. A karshe, sai suka tabbatar wa mutumin cewa duka kudaden da ake samu da kuma aikin agaji da ake yi gudummawa ne. Abin ya burge mutumin sosai, sai ya yarda ya rage farashin kuma ya ba da kyautan wake kilo 400 a kan wanda ’yan’uwan suka sake saya bayan hakan.

“Tabbaci Ne na Ƙauna ta Kwarai”

 Wata tsohuwar gwauruwa mai suna Lusu, daga kasar Laberiya tana zama da tare da ’yarta da mijinta da kuma yaransu uku. Wata rana da suke cin abinci safe da kuma yin ibada ta safiya, sai jikanta mai shekara bakwai ya lura cewa abinci ya kare gaba daya a gidan. Sai ya tambaya, “Me za mu ci?” Lusu ta ce masa ta riga ta yi addu’a cewa Jehobah ya taimaka musu kuma ta tabbata cewa zai yi hakan. Da ranar, wasu dattawa sun kira Lusu ta zo ta karba abinci. Lusu ta ce: “Jikana ya ce yanzu ya san cewa Jehobah yana jin addu’o’i domin ya ji addu’ata.”

Yara a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango suna zana hotuna don su nuna godiyarsu saboda agaji da ’yan’uwa suka ba su

 Wata mata a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango tana zama kusa da wani iyali da Shaidun Jehobah ne. Bayan da ta ga ’yan’uwa sun kawo wa iyalin abinci sai ta ce, “Bayan annobar, zan zama Mashaidiyar Jehobah domin na ga yadda suka kula da juna a wannan mawuyacin lokacin.” Sai maigidanta ya tambaye ta ya ce: “Yanzu za ki zama Mashaidiya saboda buhun shinkafa guda daya kawai?” Amma ta ce: “A’a, ba domin buhun shinkafa ba, amma shinkafan tabbaci ne na ƙauna ta kwarai.”

 Shaidun Jehobah sun iya sun ba da tallafi ’yan’uwansu ba tare da bata lokaci ba domin gudummawa da kuke bayarwa. Mun gode muku don gudummawar da kuka bayar ta wajen amfani da hanyoyi da aka tsara a donate.pr418.com.