YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA
Gine-gine da Aka Kammala Kafin Bullowar Koronabairas
1 GA NUWAMBA, 2020
Kowace shekara, dubban mutane suna yin baftisma. Don haka muna bukatar karin wuraren ibada. Sashen Gine-gine sun shirya cewa za su gina ko kuma gyara wuraren ibada fiye da 2,700 a shekarar hidima ta 2020. a
Abin takaici, annobar koronabairas ta hana su cim ma burinsu. Kwamitin Buga Littattafai na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya sa an dakatar da yawancin gine-gine da muke yi a fadin duniya, don a kāre ’yan’uwanmu kuma su bi ka’idodin da gwamnati ta kafa. Duk da haka, a shekarar hidima ta 2020, an samu an gina da kuma gyara wuraren ibada fiye da 1,700 kafin barkewar annobar koronabairas. Kari ga haka, an kammala manyan ayyukan gine-gine a ofisoshinmu fiye da 100. Ga labarin yadda ’yan’uwanmu suka amfana daga aikin gine-gine biyu da aka kammala.
Reshen ofishinmu a kasar Kamaru. Asalin reshen ofishin a birnin Douala yake, amma ya kasa kuma ya bukaci a yi masa gyara sosai. Kwamitin Buga Littattafai ya so a yi gyarar amma kudin da za a kashe wurin yin gyarar ya fi kudin ginin. Sun kuma yi bincike su ga ko zai yiwu a sayi fili a gina sabon ofishi, ko kuma a sayi wani gini a gyara shi don ya dace da abin da ake so, amma babu wanda ya yiwu a cikinsu.
Ana nan sai ’yan’uwanmu suka sami labari cewa gwamnati tana shirin gyara hanyar da ke kusa da wata Majami’ar Babban Taronmu. Hanyar za ta sa yin tafiye-tafiye ya yi sauki kuma a sami abubuwa kamar ruwa da wutar lantarki a wurin. Abin da dā ma muke nema ke nan. Saboda haka, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta amince a gina sabon reshen ofishinmu a gefen Majami’ar Babban Taron.
An yi hayar magina don su yi aiki tare da ’yan’uwan da suka ba da kansu. Hakan ya hanzarta aikin kuma ya rage kudin da aka kashe. Har an sami ragin kudi fiye da dala miliyan biyu (wajen naira 762,000,000)! Iyalin Bethel da ke Kamaru sun samu sun shiga sabon ofishinsu. Ba da dadewa ba sai aka soma annobar koronabairas.
Yanzu ’yan’uwa da suke hidima a Bethel a Kamaru suna zama da kuma aiki a wuri mai kyau, kuma sun ce sabon ofishin kyauta ce daga Jehobah. Wani dan’uwa da matarsa sun ce: “Za mu yi aiki tukuru don mu nuna godiyarmu don wannan kyautar.”
Ofishin Fassarar Yaren Tojolabal da ke kasar Meziko. Mafassaran harshen Tojolabal sun yi shekaru da dama suna aiki a reshen ofishinmu da ke kusa da Mexico City a Amirka ta Tsakiya. Amma a Birnin Altamirano da Las Margaritas ne asali ake yaren Tojolabal, kuma biranen suna da nisan wajen kilomita 1,000 (mil 620) daga inda ofishin yake! Hakan ya sa ya yi musu wuya su ci gaba da inganta fassarar da suke yi. Kari ga haka, ya yi musu wuya su samo ’yan’uwan da za a rika daukan muryoyinsu, da kuma wadanda za su taimaka da fassarar yaren Tojolabal.
Dalilan nan ne suka sa Kwamitin Rubuce-rubuce na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya ga ya dace a samo wa mafassaran ofishin fassara a yankin da ake yin yaren Tojolabal. Don a yi hakan, ofishinmu da ke Amirka ta Tsakiya ya tsai da shawarar sayan wani gini sa’an nan su gyara shi. Wannan matakin ba zai ci kudi kamar gina sabon ofishin fassara ko kuma yin haya ba.
Wani mafassari ya amfana sosai daga wannan shirin kuma ya ce: “A cikin shekaru goma da na yi ina aikin fassara a ofishinmu, ban hadu da ko iyali daya da suke yaren Tojolabal ba. Amma yanzu da aka samo mana ofishin fassara a yankin da ake yarenmu, ina yin magana da mutanen da suke yaren Tojolabal kowace rana. Hakan ya sa na koyi sabbin kalmomi da suka sa na inganta fassarar da nake yi.”
Ayyukan Gine-gine da Ake Shirin Yi a Shekarar Hidima ta 2021
A shekarar hidima ta 2021, muna shirin gina ofisoshin fassara da makarantun koyar da Littafi Mai Tsarki guda 75, idan kome ya tafi daidai. Kuma za mu ci gaba da aiki a reshen ofishinmu guda takwas, hade da sabon ginin Ramapo da ke hedkwatarmu a New York, da kuma sabon gini da za a yi don reshen ofishinmu da ke Ajantina da Italiya. Kari ga haka, muna bukatar gina sabbin Majami’un Mulki fiye da 1,000, mu gyara guda 4,000, kuma yanzu muna da wuraren ibada fiye da 6,000 da suke bukatar canji don ba su cancanta ba.
Daga ina ake samun kudin yin gine-gine da gyare-gyaren nan? Dan’uwa Lázaro González, wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Amirka ta Tsakiya, ya ba da amsar tambayar nan sa’ad da yake magana game da Ofishin Fassarar Yaren Tojolabal. Ya ce: “Ba mu da isasshen kudin tafiyar da ayyukan da muke yi a yankinmu. Saboda haka, da a ce ’yan’uwanmu a fadin duniya ba su taimaka mana ba, ba za mu iya gina ofisoshin fassara don ’yan’uwan da ke nan ba. Gudummawar da ake bayarwa a duk fadin duniya ne ya sa ya yiwu mu samar wa mafassara ofisoshin fassara a inda ake yarensu. Muna godiya sosai ga ’yan’uwanmu a duk fadin duniya don taimako da suka yi mana.” Hakika, gudummawar da kuke bayarwa don aikinmu a fadin duniya ne ya sa ya yiwu mu yi gine-ginen nan. Kuma da yawa daga cikin gudummawar ta donate.pr418.com a intane ne ake bayarwa.
a Sashen Gine-gine da ke reshen ofisoshi dabam-dabam ne yake shirya da kuma gina Majami’un Mulki da ke yankinsu. Sashen Gine-gine da ke hedkwatarmu kuma, shi ne yake zaban ayyukan gine-ginen da za a soma yi kafin wasu, kuma yana shirya yadda za a yi su.