Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Littafin Nazari da Ya Yi Dabam da Sauran

Littafin Nazari da Ya Yi Dabam da Sauran

1 GA AFRILU, 2022

 A watan Janairu 2021, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta sanar da fitowar sabon littafin nazari, wato Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! a Mene ne ka yi saꞌad da ka ji sanarwar? Wani mai suna Matthew da ke Kanada ya ce: “Na yi farin ciki! Kuma na dada farin ciki saꞌad da aka bayyana a jawabai da bidiyoyi dalilin da ya sa aka wallafa littafin da kuma yadda aka yi gwaje-gwaje a kan littafin. Na yi marmarin ganin littafin da kuma soma amfani da shi.”

 An gabatar da sabuwar hanyar gudanar da nazari da littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! Amma ba wannan ba ne kawai bambancin da ke tsakanin wannan sabon littafin da littattafan nazari da aka yi amfani da su a dā ba. Idan kana amfani da littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! za ka lura cewa ya yi dabam a hannu. Don mu san dalilin, bari mu kara koya game da yadda aka yi littafin.

Sabon Littafi da Ya Yi Dabam a Hannu

 Takarda mai laushi. Me ya sa aka yi hakan? Littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! yana da hotuna masu kaloli dabam-dabam fiye da 600! Hakan ya fi na littafin Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki kusan sau goma. Sabon littafin yana da wuraren da babu rubutu ko hotuna a shafuffukansa. Wadannan abubuwa biyu suna jawo matsala: Idan takardar ba ta da kauri, za a iya ganin hotuna da ke bayan shafin. Don kada hakan ya faru, ꞌyanꞌuwa da ke aiki a Sashen Buga Littattafai a Hedkwata da ke Wallkill a jihar New York a Amirka sun gwada takardu dabam-dabam guda hudu da muke amfani da su yanzu a wurin da muke buga littattafanmu. Kwamitin Rubuce-rubuce na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun bincika kowanne kuma suka zabi takarda da ba a ganin rubutu da ke bayansa. Wannan takardar ta fi wadda muka yi amfani da ita a yawancin littattafanmu a dā tsada. Amma yin amfani da ita yana ba dalibai damar karanta kowane shafi na littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! ba tare da hotuna da ke bayan shafin ya raba hankalinsu ba.

Shafi da ke hannun dama yana nuna irin takardar da aka yi amfani da shi wajen buga littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!

 Bangon ya yi dabam. Bangon sabon littafin ya yi dabam da wadanda muka yi amfani da su a littattafanmu domin an kāre bango gaba da bayan da wani abu kamar leda. A sabon littafin mun yi amfani da wani abu kamar leda da ke sa hotunan littafin ya fito da kyau maimakon yin amfani da wanda aka saba yin amfani da shi. Wannan abin yana kāre littafin don kada ya lalace saboda yawan amfani. Wannan irin ledar da aka kāre littafin da shi yana da tsada sosai fiye da wanda ake amfani da shi a dā. Saboda haka, ofisoshin Shaidun Jehobah da yawa sun hada kai don su sayi wannan irin ledar mai kyau da ba shi da tsada sosai.

Ana saka wani abu kamar leda a bangon littafin

 Me ya sa aka zabi wadannan kayayyaki masu tsada? Wani danꞌuwa da ke aiki a Sashen Buga Littattafai a Hedkwata ya bayyana cewa: “Muna so wannan littafin ya kasance da kyau ko da mutum ya yi amfani da shi sau da yawa.” Wani danꞌuwa mai suna Eduardo da ke aiki a Sashen Buga Littattafai a reshen ofishi da ke Brazil ya ce: “Mun yi farin cikin ganin yadda kungiyar Jehobah ta yi amfani da kayayyaki masu kyau don ta sa wannan littafin ya yi kyau, ya rika dadewa da kuma dadin tabawa. Duk da haka, sun yi amfani da gudummawar da ake bayarwa da kyau.”

Buga Littattafai a Lokacin Annobar Korona

 Mun soma buga littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! a watan Maris 2021. Wannan lokacin annobar korona ne kuma hakan ya jawo matsaloli. Tun da yake an rufe dukan Reshen Ofisoshi, ꞌyanꞌuwa masu zuwa aiki a Bethel daga gidajensu ba su iya taimaka mana a a wurin buga littattafanmu ba. Kuma ba mu iya gayyaci ꞌyanꞌuwa su zo aiki a Bethel ba. Hakan ya sa wasu wuraren buga littattafanmu ba su da isashen maꞌaikata, kuma an rufe wasu na dan lokaci domin gwamnati ta saka takunkumi.

 Ta yaya aka magance wadannan matsalolin? Saꞌad da aka soma aiki a wurin buga littattafanmu, an tura wasu ꞌyanꞌuwa maza da mata da suke aiki a wasu wurare a Bethel don su zo su taimaka a wannan sashen na dan lokaci. Wani danꞌuwa mai suna Joel da ke aiki a Sashen Buga Littattafai a Hedkwata ya ce: “Kasancewa a shirye su koyi sabon aiki da kuma halinsu na son taimakawa ya sa mu cim ma wannan aikin.”

 Duk da kalubalen da muka fuskanta, mun riga mun buga miliyoyin littattafan Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! Mun bukaci kayan aiki dabam-dabam, hakan ya kunshi kayan buga littattafai da wani abu kamar leda don rufe bangon, da takarda da tawada da kuma gam. A watanni biyar na farko da muka soma buga littafin, mun kashe fiye da dala miliyan 2 da dari uku wajen sayan kayayyaki kawai. Don mu rage kashe kudi, mun buga adadin littattafai da ikilisiyoyi suke bukata kadai.

“Aiki Ne Mai Kyau”

 Ta yaya masu koyar da Littafi Mai Tsarki da dalibansu suke ji game da wannan sabon littafin? Wani danꞌuwa mai suna Paul a Australiya ya ce: “Ina jin dadin nazari da littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!, har nakan yi farin ciki sosai idan na yi tunanin yin nazari da mutane. Yadda aka shirya littafin yana da kyau sosai, kamar kuna tattaunawa ne da dalibin. Littafin na dauke da bayanai masu kyau da tambayoyi masu ratsa zuciya, da bidiyoyi da hotuna da taswirori masu kyau da kuma makasudai da dalibin zai kafa. Aiki ne mai kyau da ke motsa ni in inganta yadda nake koyarwa.”

 Wani dalibi a Amirka ya ce: “Ina son wannan sabon littafin sosai. Hotunan suna taimaka min in fahimci muhimman darussan. Bidiyoyin suna ratsa zuciyata kuma suna motsa ni in dauki mataki.” Wannan dalibin yana nazari sau biyu a mako kuma yana halartan taron ikilisiya a kai a kai.

 Har ila za a kara buga littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! a harsuna da yawa. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ba da izini a wallafa wannan littafin a harsuna 710. Hakan ya fi na littafin Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? sau 340!

 Ta yaya muke samun kudin buga wadannan littattafan? Ta wurin ba da gudummawar kudi, mutane da yawa suna yin hakan a naꞌurarsu ta wurin donate.pr418.com. Muna godiya don gudummawar da kuke bayarwa, hakan yana taimaka mana mu wallafa littattafan nazarin Littafi Mai Tsarki don wadanda suke so su koya game da Jehobah kuma su ji dadin rayuwa “har abada.”​—Zabura 22:26.

a An fitar da wannan littafin a shirye-shiryen JW da aka yi a lokacin taron shekara shekara.