Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Yadda Ake Taimaka wa Masu Bukata

Yadda Ake Taimaka wa Masu Bukata

1 GA OKTOBA, 2020

 Shaidun Jehobah suna yin ayyuka masu muhimmanci don su taimaka wa mutane a kasashe fiye da 200. Amma a cikin kasashen nan, kasashe 35 ne kawai suke ba da gudummawar da ta isa ta biya bukatunsu. Ya ake samun kudaden da ake kashewa wajen yin ayyukanmu a kasashen da ba su da kudi sosai?

 Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu sukan duba abubuwan da Shaidun Jehobah suke bukata a duk duniya. Sa’an nan su kasafta yadda za a kashe kudaden da ake samuwa, kuma a yi amfani da su yadda ya dace. Idan kudin da aka samu a wani reshen ofishinmu ya isa su biya bukatunsu har ya rage, sukan ba da kudin don wasu kasashe su amfana. Irin abin da Kiristoci a karni na farko suka yi ke nan, sun taimake juna domin ‘kome ya zama daidai.’ (2 Korintiyawa 8:14) Sun yi amfani da abin da ya rage musu sun taimaki ’yan’uwansu da ba su da shi.

 Yaya ’yan’uwan da suka sami tallafi daga wasu kasashe suke ji? A kasar Tanzaniya yawancin mutane ba sa samun abin da ya kai naira 760 a rana. Kudin da ’yan’uwanmu suka bayar daga wata kasa ne aka yi amfani da shi wajen gyara Majami’ar Mulkin da Ikilisiyar Mafinga take. Ikilisiyar ta tura wasikar godiya tana cewa: “Bayan gyarar, mutanen da suke zuwa taronmu sun karu! Mun gode wa kungiyar Jehobah da kuma ’yan’uwanmu a fadin duniya, gudummawarsu ne ya sa an samu an gyara mana wurin ibadarmu.”

 Wasu ’yan’uwanmu a kasar Sri Lanka sun yi fama da karancin abinci sakamakon annobar koronabairas. Wasu daga cikin ’yan’uwan nan su ne Imara Fernando da danta karami mai suna Enosh. Amma gudummawa da aka samu daga wasu kasashe ta sa an ba su tallafi. ’Yar’uwar da danta sun tura katin godiya suna cewa: “Mun gode wa ’yan’uwan da suka nuna mana kauna a wannan mawuyacin lokacin. Mun gode Allah muna da ’yan’uwa a ko’ina a duniya, kuma muna rokon Jehobah ya ci gaba da taimaka wa dukan ’yan’uwanmu a wadannan kwanaki na karshe.”

Imara da Enosh Fernando

 ’Yan’uwanmu a ko’ina suna kokari wajen ba da gudummawa don su tallafa wa ’yan’uwansu da abin da suke da shi. Alal misali, Enosh ya yi wani karamin asusu da zai rika tara kudi don ya ba da gudummawa. Yana so a yi amfani da shi wajen tallafa wa mabukata. ’Yar’uwa Guadalupe Álvarez daga Meziko ma tana jin dadin ba da gudummawa. Tana zama a bangaren Meziko da mutane kalilan ne suke samun mafi karancin albashi da gwamnati take biya, da yawa ma ba su da aikin da ake biyan su albashi. Duk da haka, tana ba da gudummawa iya gwargwadon karfinta. Ta rubuta cewa: “Na gode wa Jehobah don alherinsa da kaunarsa. Na san za a hada gudummawata da na wasu don a taimaka wa ’yan’uwan da suke da bukata.”

 Ofisoshinmu da suke tura kudade zuwa wuraren da akwai bukata suna farin cikin yin hakan. Wani memban Kwamitin Reshen Ofishinmu da ke Brazil, mai suna Anthony Carvalho ya ce: “Mun yi shekaru da dama ba ma samun isasshen kudin tafiyar da ayyukan da ake yi a kasarmu sai da taimakon wasu kasashe. Tallafin da muka yi ta samuwa ne ya taimaka mana mun sami karuwar masu shela sosai. Amma yanzu kudin da muke samuwa ya karu, har muna iya tallafa wa wasu kasashe. ’Yan’uwan da ke Brazil sun san cewa aikin wa’azin da muke yi, a duk fadin duniya ne, don haka, suna iya kokari su ga sun taimaka da duk abin da suke da shi.”

 Me Shaidun Jehobah za su iya yi don su taimaka wa ’yan’uwansu da suke da bukata? Ba sai sun tura kudi zuwa reshen ofishinmu da ke wata kasa ba, amma za su iya yin hakan ta wajen ba da gudummawa don aikinmu a fadin duniya. Mutum zai iya saka gudummawarsa a akwatin ba da gudummawa na ikilisiya da aka rubuta “Gudummawa na Aikin Dukan Duniya” ko kuma ya tura ta donate.pr418.com a intane. Mun gode muku sosai don gudummawarku.