Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 102

“Mu Taimaki Marasa Karfi”

“Mu Taimaki Marasa Karfi”

(Ayyukan Manzanni 20:35)

  1. 1. Kowannenmu na fama

    Da kasawarsa.

    Amma Jehobah Allah,

    Yana ƙaunar mu.

    Yana nuna jinƙai,

    Har da ƙauna sosai.

    Mu nuna ƙaunar nan ga,

    Marasa ƙarfi.

  2. 2. Wasu bangaskiyarsu,

    Ta soma sanyi.

    Amma furuci mai kyau,

    Zai taimake su.

    Allah na ƙarfafa

    Ƙaunatattun nan fa.

    Mu nuna muna son su,

    Mun damu da su.

  3. 3. Maimakon mu guje su,

    Mu kusace su.

    Mu ƙarfafa su sosai

    Da furucinmu.

    Mu riƙa ƙoƙarta,

    Mu ƙaunace su fa.

    Yayin da muke hakan,

    Za su yi ƙarfi.

(Ka kuma duba Isha. 35:​3, 4; 2 Kor. 11:29; Gal. 6:2.)