Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 116

Muhimmancin Yin Alheri

Muhimmancin Yin Alheri

(Afisawa 4:32)

  1. 1. Jehobah muna yabon ka sosai

    Da dukan zucinmu,

    Domin kirkinka da alherinka,

    Duk da kai Maɗaukaki ne.

  2. 2. Ubangijinmu yana tausaya

    Wa duk gajiyayyu.

    Ƙaunarsa da kuma alherinsa

    Suna sanyaya zuciya.

  3. 3. Jehobah Allah da Yesu Kristi

    Suna yin alheri.

    Yin koyi da su zai sa mu zama

    Masu alheri da jinƙai!

(Ka kuma duba Mik. 6:8; Mat. 11:​28-30; Kol. 3:12; 1 Bit. 2:3.)