Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 140

Za Mu Yi Rayuwa Har Abada!

Za Mu Yi Rayuwa Har Abada!

(Yohanna 3:16)

  1. 1. Za mu more aljanna

    Da Jehobah zai kawo.

    Ba ɓacin rai, ba cuta,

    Sai dai kwanciyar rai.

    (AMSHI)

    Mu yi waƙar yabo

    Domin albarkun nan!

    Mu yi ɗokin kasance

    “A cikin Aljanna!”

  2. 2. Dukanmu a Aljanna

    Za mu zama matasa.

    Za mu daina jin tsoro,

    Har da yin kuka ma.

    (AMSHI)

    Mu yi waƙar yabo

    Domin albarkun nan!

    Mu yi ɗokin kasance

    “A cikin Aljanna!”

  3. 3. Za mu riƙa ɗaukaka

    Allahnmu a Aljanna.

    Har abada, za mu yi

    Wa Allah godiya.

    (AMSHI)

    Mu yi waƙar yabo

    Domin albarkun nan!

    Mu yi ɗokin kasance

    “A cikin Aljanna!”

(Ka kuma duba Ayu. 33:25; Zab. 72:7; R. Yoh. 21:4.)