Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 158

“Ba Zai Yi Latti Ba!”

“Ba Zai Yi Latti Ba!”

(Habakkuk 2:3)

  1. 1. Dukan duniya

    na da kyau sosai,

    Ta nuna cewa

    kai mai hakuri ne.

    Alkawuranka

    ba sa canjawa,

    Za ka cika su,

    “ba zai yi latti ba.”

    (AMSHI)

    Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,

    Don mu shiga Aljanna.

    Madaukaki, Uba,

    ka kawo Mulkinka.

    Mun san zai zo,

    ba shakka,

    Ba zai fasa ba!

  2. 2. Muna marmarin

    ganin lokacin

    Da amintattu

    da ke kabarbura,

    Za su sami rai

    a duniyar nan.

    Mu jimre sosai

    don mu marabce su.

    (AMSHI)

    Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,

    Don mu shiga Aljanna.

    Madaukaki, Uba,

    ka kawo Mulkinka.

    Mun san zai zo,

    ba shakka,

    Ba zai fasa ba!

  3. 3. Kana tattara

    masu kaunar ka

    Don su bauta ma,

    su sami albarka.

    Muna waꞌazi

    da himma sosai.

    Yin hakan na sa

    mu yi kusa da kai.

    (AMSHI)

    Muna roko Uba, ka ba mu jimiri,

    Don mu shiga Aljanna.

    Madaukaki, Uba,

    ka kawo Mulkinka.

    Mun san zai zo,

    ba shakka,

    Ba zai fasa ba!

    Uba, ka sa mu jimre!

(Ka kuma duba Kol. 1:11.)