WAƘA TA 23
Jehobah Ya Soma Sarautarsa
(Ru’ya ta Yohanna 11:15)
-
1. Mu yabi Yesu Kristi,
Don ya soma sarauta.
Kristi shi ne Sarkin Mulkin Allah.
Duk mu ta da muryarmu.
Mu riƙa yabon Allah.
An ba wa Mai Cetonmu,
Yesu, sarauta.
(AMSHI)
Me Mulkin Allahnmu zai kawo?
Gaskiya har da adalci.
Me kuma Mulkin nan zai kawo?
Rai mai cike da jin daɗi.
Mu yabi Jehobah Allah,
Mai ƙauna da aminci.
-
2. A yaƙin Armageddon,
Ɗan Allah ne ja-gora.
Za a halaka ayyukan Shaiɗan.
Mu je mu yi wa’azi.
Mu yi shela ga kowa,
Don su soma bauta
wa Allah Jehobah.
(AMSHI)
Me Mulkin Allahnmu zai kawo?
Gaskiya har da adalci.
Me kuma Mulkin nan zai kawo?
Rai mai cike da jin daɗi.
Mu yabi Jehobah Allah,
Mai ƙauna da aminci.
-
3. Muna ƙaunar Sarkinmu,
Muna yabon sa sosai.
Allahnmu ne ya naɗa shi sarki.
Ku bauta wa Jehobah;
Don ku sami albarka.
Ba da daɗewa ba
zai soma sarauta.
(AMSHI)
Me Mulkin Allahnmu zai kawo?
Gaskiya har da adalci.
Me kuma Mulkin nan zai kawo?
Rai mai cike da jin daɗi.
Mu yabi Jehobah Allah,
Mai ƙauna da aminci.
(Ka kuma duba 2 Sam. 7:22; Dan. 2:44; R. Yoh. 7:15.)