WAƘA TA 26
Ka Yi Domin Ni
(Matta 25:34-40)
-
1. Waɗansu tumaki mabiyan Yesu ne,
suna yin aiki tare da shafaffu.
Aikin da suke yi
don su taimake su,
Na sa Yesu murna, zai sāka musu.
(AMSHI)
“In kun ƙarfafa su, kun ƙarfafa ni.
In kun yi domin su, kun yi domin ni.
Ayyukan da kun yi kun yi domin ni.
Kun yi domin su, kun yi domin ni.
In kun yi domin su, kun yi domin ni.”
-
2. “Kun ciyar da ni fa, kun shayar da ni ma,
kun biya mini dukan bukatuna.”
Za su gaya wa Sarkin:
“A yaushe ke nan?”
Shi zai gaya musu dalilin hakan:
(AMSHI)
“In kun ƙarfafa su, kun ƙarfafa ni.
In kun yi domin su, kun yi domin ni.
Ayyukan da kun yi kun yi domin ni.
Kun yi domin su, kun yi domin ni.
In kun yi domin su, kun yi domin ni.”
-
3. “Kun nuna aminci da kuma nagarta,
don kun yi wa’azi da ʼyan’uwana.”
Sarkin zai ce wa waɗansu
tumakinsa:
“Ku ji daɗin duniya har abada.”
(AMSHI)
“In kun ƙarfafa su, kun ƙarfafa ni.
In kun yi domin su, kun yi domin ni.
Ayyukan da kun yi kun yi domin ni.
Kun yi domin su, kun yi domin ni.
In kun yi domin su, kun yi domin ni.”
(Ka kuma duba Mis. 19:17; Mat. 10:40-42; 2 Tim. 1:16, 17.)