WAƘA TA 33
Mu Mika Dukan Damuwarmu ga Jehobah
(Zabura 55)
-
1. Ina so in kusace ka,
Ya Jehobah Allahna.
Allah ka taimaka mini
Don in daina jin tsoro.
(AMSHI)
Ka dogara ga Jehobah,
Zai kula da kuma cece ka.
Allah zai kāre ka kullum
Don shi mai aminci ne.
-
2. Da a ce zan iya tashi,
Zan guje wa mugaye.
Zan nisanta kaina da su
Domin kar su kama ni.
(AMSHI)
Ka dogara ga Jehobah,
Zai kula da kuma cece ka.
Allah zai kāre ka kullum
Don shi mai aminci ne.
-
3. Ƙarfafa daga Jehobah,
Na kwantar mana da rai.
Zai taimake mu mu jimre,
Shi Allah ne mai ƙauna.
(AMSHI)
Ka dogara ga Jehobah,
Zai kula da kuma cece ka.
Allah zai kāre ka kullum
Don shi mai aminci ne.
(Ka kuma duba Zab. 22:5; 31:1-24.)