WAƘA TA 52
Alkawarinmu ga Jehobah
(Ibraniyawa 10:7, 9)
-
1. Allah Jehobah ne ya yi
Sammai da duniya.
Shi ne ya halicci kome,
Duk ayyukansa ne.
Ya ba da rai ga ’yan Adam
Da kuma dabbobi.
Shi ne Allahn da ya cancanci
Yabo da kuma bauta.
-
2. Ɗan Allah ya yi baftisma
Domin amincinsa.
Ya ce wa Mahaliccinsa:
‘Na zo yin nufinka.’
Sa’ad da ya yi baftisma
Ya zama shafaffe.
Ya yi addu’a ga Allahnsa:
‘Uba a yi nufinka.’
-
3. Mun zo gabanka, Jehobah,
Domin mu bauta ma.
Mun ba ka duk rayuwarmu
Don mu yi nufinka.
Ɗanka ya zo duniyar nan
Domin ya fanshe mu.
Ko mun mutu ko muna raye,
Mu naka ne koyaushe.
(Ka kuma duba Mat. 16:24; Mar. 8:34; Luk. 9:23.)