WAƘA TA 72
Mu Yada Gaskiya Game da Mulkin Allah
(Ayyukan Manzanni 20:20, 21)
-
1. A dā muna cikin duhu
Shaiɗan ya makantar da mu.
Sai Jehobah Allahnmu,
Ya koya mana gaskiya.
Mun koyi nufin Allahnmu,
Mun soma wa’azin Mulki,
Mun yaɗa ɗaukakarsa
Kuma muna tsarkake sunansa.
Muna wa’azi ga kowa,
Gida-gida da kan titi.
Kullum muna ƙoƙartawa
Don mu yi wa’azi sosai.
Yin wa’azi a ko’ina
Na sa a bauta wa Allah,
Mu riƙa ƙoƙartawa
Har sai Jehobah ya ce ya isa.
(Ka kuma duba Josh. 9:9; Isha. 24:15; Yoh. 8:12, 32.)