Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 77

Haske a Duniya Mai Duhu

Haske a Duniya Mai Duhu

(2 Korintiyawa 4:6)

  1. 1. A cikin wannan duniyar,

    Haske ya haskaka.

    Kamar da wayewar gari

    Haske ya kasance.

    (AMSHI)

    Haske cikin duhu

    Shi ne bisharar Mulki

    Da muke yi a yau.

    Kamar hasken rana

    Ta sa mu ga albarka

    A ko’ina.

  2. 2. Mu ta da masu yin barci

    Don babu lokaci.

    Muna so mu koyar da su

    Don su sami ceto.

    (AMSHI)

    Haske cikin duhu

    Shi ne bisharar Mulki

    Da muke yi a yau.

    Kamar hasken rana

    Ta sa mu ga albarka

    A ko’ina.

(Ka kuma duba Yoh. 3:19; 8:12; Rom. 13:​11, 12; 1 Bit. 2:9.)