WAƘA TA 97
Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu
(Matta 4:4)
-
1. Kalmar Allah na ba da rai
Mai inganci sosai.
Kalmar tana da tamani,
Fiye da abinci.
Muna cin amfanin Kalmar,
Yau da kuma gobe.
(AMSHI)
Wajibi ne mu karanta
Kalmar Allah sosai.
Karanta Kalmar za ta sa
Mu amfana sosai.
-
2. Kalmar Allah na sa mu san
Labaran mutane,
Mutane amintattu fa,
Masu gaba gaɗi.
Karanta duk labarinsu
Yana ƙarfafa mu.
(AMSHI)
Wajibi ne mu karanta
Kalmar Allah sosai.
Karanta Kalmar za ta sa
Mu amfana sosai.
-
3. Koyaushe in mun karanta
Kalmar Maɗaukaki,
Tana ƙarfafa mu sosai,
Tana sa mu jimre.
In mun daraja Kalmarsa,
Za mu sami bege.
(AMSHI)
Wajibi ne mu karanta
Kalmar Allah sosai.
Karanta Kalmar za ta sa
Mu amfana sosai.
(Ka kuma duba Josh. 1:8; Rom. 15:4.)