Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna da Shi da Kaunarsa

Ka Tuna da Shi da Kaunarsa

Ka Saukar:

  1. 1. In na ga ikon Allah a sama da kasa . . .

    Allahnmu ya yi abubuwa da ke kwantar min da rai.

    Shi ya sa yake da kyau mu nemi lokaci

    Mu dan bar ayyukanmu na yau da gobe, don mu dan shakata.

    (AMSHI)

    Mu kalli halittunsa, mu gode wa Allah

    Don kaunar da yake nunawa.

    Komen kankancin abin da ya yi, zai sa

    Mu tuna da shi,

    Da kaunarsa.

  2. 2. Da dare akwai taurari, wata na haskawa.

    Allah ne ya yi su domin mu amfana, kar mu yi watsi da su.

    Domin za su sa mu tuna cewa Allah na nan.

    Za su sa mu jimre komen matsaloli, don Jehobah yana nan.

    (AMSHI)

    Mu kalli halittunsa, mu gode wa Allah

    Don kaunar da yake nunawa.

    Komen kankancin abin da ya yi, zai sa

    Mu tuna da shi

    Da kaunarsa.

    Da kaunarsa,

    Da kaunarsa.

    (AMSHI)

    Mu kalli halittunsa, mu gode wa Allah

    Don kaunar da yake nunawa.

    Komen kankancin abin da ya yi, zai sa

    Mu tuna da shi

    Da kaunarsa.

    (KARASHEN WAKAR)

    Ka dakata don ka iya kallon

    Ayyukan Allah.

    Kallon halittu zai sa ka huta,

    Domin ka tuna da shi

    Da kaunarsa.