Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mu Sasanta

Mu Sasanta

Ka Saukar:

  1. 1. Na riƙe shi a zuciya

    Domin ya min wani laifi.

    Jehobah ka taimaka min

    In gafarta. Hakan zai fi,

    Zai ban sauƙi.

    (AMSHI)

    Yanzu ba ɓata lokaci.

    Zan yi iya ƙoƙarina

    In je domin mu sasanta.

    Mu sasanta, mu sasanta.

  2. 2. Ko da me ya yi zan yafe.

    Jehobah na gafartawa.

    Ni ma zan yi koyi da shi.

    Zan gafarta, zan bar fushi;

    Ƙauna ke nan!

    (AMSHI)

    Yanzu ba ɓata lokaci.

    Zan yi iya ƙoƙarina

    In je domin mu sasanta.

    Mu sasanta, mu sasanta.

  3. 3. Aboki, na zo

    Mu yi zama kamar na dā.

    Kar mu tuna baya.

    Ni naka ne, kai nawa ne.

  4. 3. Allah yana son dukanmu.

    Yana so mu zauna tare.

    Yafewa zai sa ni murna,

    Shi ya sa zan yafe masa

    In bar kome.

    (AMSHI)

    Yanzu ba ɓata lokaci.

    Zan yi iya ƙoƙarina

    In je domin mu sasanta.

    Mu sasanta, mu sasanta,

    Mu sasanta, mu sasanta.

    Zan je mu shirya.